Dalilin dayasa muka shiga damuwa akan Buhari, APC – Sabuwar PDP

Dalilin dayasa muka shiga damuwa akan Buhari, APC – Sabuwar PDP

- Mambobin sabuwar PDP wadanda suka koma APC suka kuma taimakawa jam’iyyar taci zabe a shekarar 2015, sun bayyana rashin godiya da shugaba Buhari yake nuna masu da jam’iyyar

- Mambobin wadanda suka dawo daga jam’iyyar PDP zuwa APC a shekarar 2013 sune tsohon gwamnan jiha Sokoto liyu Wamako, na Kano Rabi’u Kwankwaso, na Kwara Abdulfatah Ahmed, na Adamawa, Murtala Nyako da kuma na Rivers Rotimi Amaechi

- ‘Yan PDP a ranar Laraba sun rubutawa ciyaman na jam’iyyar APC na tarayya wasika, Jhn Odigie-Oyegun, inda suka bukaci ganawa da shugaban kasa cikin kwanaki bakwai

Mambobin sabuwar PDP wadanda suka koma APC suka kuma taimakawa jam’iyyar taci zabe a shekarar 2015, sun bayyana rashin godiya da shugaba Buhari yake nuna masu da jam’iyyar, duk da kokarin da sukeyi masu.

Mambobin wadanda suka dawo daga jam’iyyar PDP zuwa APC a shekarar 2013 sune tsohon gwamnan jihar Sokoto liyu Wamako, na Kano Rabi’u Kwankwaso, na Kwara Abdulfatah Ahmed, na Adamawa, Murtala Nyako da kuma na Rivers Rotimi Amaechi.

Dalilin dayasa muka shiga damuwa akan Buhari, APC – Sabuwar PDP

Dalilin dayasa muka shiga damuwa akan Buhari, APC – Sabuwar PDP

‘Yan PDP a ranar Laraba sun rubutawa ciyaman na jam’iyyar APC na tarayya wasika, John Odigie-Oyegun, inda suka bukaci ganawa da shugaban kasa cikin kwanaki bakwai.

Bayan haka a sun tanasar da Odigie-Oyegun a cikin wata wasika da suka fitar ta hanyar TheCable, tare da sanya hannun Messrs Baraje da Oyinlola, na cewa dawowarsu jam’iyyar ba wai martabar jam’iyyar kadai ta karu ba, amma sai da suka tabbatar da cewa jam’iyyar ta samu nasara a zabe.

KU KARANTA KUMA: Yakasai, Mantu, da kuma wasu shugabanin arewa sun gana da Saraki akan zaben 2019

Sun kara da cewa wasu cikin gwamnonin an basu wani aiki na kawo jihohinsu ga jam’iyyar ta APC a zaben shekarar 2015, kuma sunyi hakan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel