Yakasai, Mantu, da kuma wasu shugabanin arewa sun gana da Saraki akan zaben 2019

Yakasai, Mantu, da kuma wasu shugabanin arewa sun gana da Saraki akan zaben 2019

- Manyan jagororin arewa a karkashin kungiyar shuwagabannin arewa da kuma masu ruwa da tsaki a arewa sun gana da shugaban majalisa Bukola Saraki

- Sun tattauna ne game da lamurran da suka shafi inda arewa ta nufa kafin zuwan zaben 2019

- Wadanda suka halarci taron sun hada da Alhaji Tanko Yakasai, Ibrahim Mantu, Dr. Bello Halilu, tsohon gwamnan Niger Mu’azu Babangida Aliyu da kuma tsohon gwamnan jihar Kogi Idris Wada

Manyan jagororin arewa a karkashin kungiyar shuwagabannin arewa da kuma masu ruwa da tsaki a arewa sun gana da shugaban majalisa Bukola Saraki.

Sun tattauna ne game da lamurran da suka shafi inda arewa ta nufa kafin zuwan babban zabe na shekarar 2019.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Alhaji Tanko Yakasai, Ibrahim Mantu, Dr. Bello Halilu, tsohon gwamnan Niger Mu’azu Babangida Aliyu da kuma tsohon gwamnan jihar Kogi Idris Wada, sun gudanar da taron a wani bangare na majalisa.

Sauran wadanda suka halarci taron sune tsohon ministan birnin tarayya Bala Mohammed da Abba Gana, tsohon ministan al’amuran mata Hajiya Inna Ciroma, Dr. Umar Ardo, Hajia Zainab Maina, Dr. Mamman Shata, da kuma Sanata Joseph Waku.

KU KARANTA KUMA: Na cancanci yabo ba wai kushewa ba saboda na kashewa ofishin EFCC N24bn - Magu

Saraki a jawabin da aka bawa manema labarai yace daga ofishinsa ya bukaci shuwagabannin arewa dasu hada hannu wurin taya gwamnatin tarayya magance matsalar kisan mutane da akeyi babu wani dalili a fadin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel