Daya daga cikin 'yan fashin offa ya shigo hannu, ashe tsohon dan sanda ne

Daya daga cikin 'yan fashin offa ya shigo hannu, ashe tsohon dan sanda ne

Jami'an yan sanda na musamman da babban sufetan yan sanda ya aike jihar Kwara sunyi nasarar kama daya daga cikin wandanda ake zargi da yin fashi a bankuna da kashe-kashen mutane a garin Offa da ke jihar Kwara.

Wanda aka zargin mai suna Michael Adikwu dai tsohon jami'in hukumar Yan sandan jihar Kwara ne wanda aka sallama daga aiki bayan an same shi da laifin hadin baki wajen taimakawa wasu wadanda ake zargi da fashi tserewa daga hannun yan sanda.

'Yan sanda sunyi nasarar cafke daya daga cikin wadanda sukayi fashin Offa

'Yan sanda sunyi nasarar cafke daya daga cikin wadanda sukayi fashin Offa

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, kafin sallamarsa daga aiki, Adikwu jami'i ne tare da sashi na musamman don kiyaye fashi da makami na hukumar Yan sandan.

KU KARANTA: Farfesa Sagay ya kare Sufeta Idris, ya ce Sanatocin Najeriya ne makiyan demokradiyya

Rahotanni sun bayyana cewa an gurfanar da Adikwu a kotu inda aka tura shi gidan yari na tsawon shekaru uku amma daga baya ya fice kuma ya fara aikata fashi da makami tare da wasu abokansa.

Tawagar fitaccen dan sanda Abba Kyari ne suka cafke Adikwu ne a ranar Talata a garin Kwara bayan sun sami bayanan sirri daga mutane wanda suka gane fuskar sa cikin hotunan mutanen da ake nema ruwa a jallo saboda aikata fashi da makamin.

Adikwu da tawagar sa sunyi fashin ne a ranar 5 ga watan Afrilu inda suka kashe a kalla mutane 50 cikin har da yan sanda guda tara.

Duk da cewa hukumar yan sanda ta kama mutane 20 da ake zargi da hannu cikin fashin, gwamnatin jihar Kwara ta sanya tukwuicin naira miliyan 5 ga duk wanda ya taimaka da bayannan yadda za'a kamo su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel