Farfesa Sagay ya kare Sufeta Idris, ya ce Sanatocin Najeriya ne makiyan demokradiyya

Farfesa Sagay ya kare Sufeta Idris, ya ce Sanatocin Najeriya ne makiyan demokradiyya

Shugaban kwamitin bawa shugaban kasa shawarwari a kan kawar da rashawa (PACAC), Farfesa Itse Sagay ya cacaki Majilisar Dattawa saboda sanarwar da ta fitar na ayyana babban sufetan Yansanda Najeriya, Ibrahim Idris, a matsayin makiyin demokradiyya.

Sufeta Janar na hukumar Yansandan yayi burus da gayyatar da majalisar dattawa tayi masa har sau uku wanda hakan ne ya janyo majalisar tayi masa wannan mumunnan shaida.

Ku ne makiyan demokradiya na asali: Sagay ya fadawa Majlisar Dattawa

Ku ne makiyan demokradiya na asali: Sagay ya fadawa Majlisar Dattawa

KU KARANTA: Za'ayi gwajin kwakwalwa ga matasan da ke son shiga aikin dan sanda

Jaridar Daily Independent ta ruwaito cewa Sagay ya ce shugaban yan sandan ya aike da mataimakin sufeta janar don ya wakilce shi a gaban majalisar.

Sagay ya ce yadda Sanatocin su ka yi watsi da aikin su don su tafi asibiti ziyarar abokin aikinsu wanda ake tuhuma da aikata laifi shine ainin kiyaya da demokradiyya.

Kalamansa: "Ni fa ban amince ba, bana tunanin sufetan yan sanda ya gabatar da kansa a matsayin makiyin demokradiyya."

"Irin hallayen yan majalisan ne abin tsoro ga demokradiyyar mu duba da yadda su ka yi watsi da aikin su a majalisa suka tafi asibiti don nuna goyon baya ga takwaransu da ake tuhuma da aikata laifi. Wannan shine alamar watsi da demokradiyya".

"Sun dade suna wuce gona da iri wajen gudanar da ayyukansu kuma hakan ya nuna mana cewa har yanzu basu goge ba wajen gudanar da ayyukansu a karkashin mulkin demokradiyya. Wannan shine abinda na lura dashi."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel