Siyasa: Bambanci tsakanin Santsi da Tabo, ko yaya abin yake a yau?

Siyasa: Bambanci tsakanin Santsi da Tabo, ko yaya abin yake a yau?

- Tabo shi ake kira Conservatism, watau ra'ayin mazan jiya, Santsi shine Liberalism, watau sauyi

- A Najeriya ana gwabzawa sosai tsakayin bangarorin biyu, inda akan sami sa toka sa katsi

- A yanzu matasa sunfi son santsi, inda dattijai kan nuna a zauna a tabo

Siyasa: Bambanci tsakanin Santsi da tabo, ko yaya abin yake a yau?
Siyasa: Bambanci tsakanin Santsi da tabo, ko yaya abin yake a yau?

Santsi, shine tsarin siyasa dake taffiya da zamani, yakan sauya ra'ayi, muddin sabbin bayanai, ilimi, ko yanayi ya sauya, domin a tafi daidai da zamani, a kuma daidaita fahimta.

Shi kuwa tsarin siyasar tabo, tsari ne na a rike ra'ayin jiya, ko ra'ayin bara, ko a rike ra'ayin shekaru 1000 ma da suka wuce, babu canji, kome wahalarsa, komai jahilcin da wadanda suka dabbaqa shi suke ciki, a zauna akai, koda kuwa ilimi da hankali ya nuna an tafka kuskure.

DUBA WANNAN: An jefe wata mata har lahira

Shi tsarin Santsi, samari da masu ilimi, da masu fahimtar jiya da yau da gobe kan so shi, masu binsa sun zaga al'ummu da duniya, don haka fahimmtarsu ta fadada har suna iya fahimtar maslaha da iyar da sauyi domin ci gaba.

Masu bin tabo kuwa, dattijai ne, wadanda ko dai saboda tsoron sauyi ka-iya kore al'adu na gargajiya, ko wasu dabi'u da adddinan zamanin da suka qirqira ko suka sanya bisa doka, wannan kansa su qi yarda a sami sauyi, su cije sai lallai kafafu da duga-dugai sun tabbata kan wannan ra'ayi, ko da kuwa ba daga kasar da suke aka faro shi ba.

Misalin Santsi, shine A ajje kiyayya a tsakanin jama'a da a da basu ga-maciji da juna, ko don addinanci, kabilanci ko siyasa ko bangaranci, a rungumi juna a sanya danba ta yarjejeniya da fahimtar juna.

Misalin Tabo shine, ace tunda haka iyaye da kakanni suka yi, muma dole haka zamuyi, domin su suka iya, su suka fahimta, sun san dalilai na dabbaqa aqidun da muke kai, tun tali-tali haka ake yi, canji ka 'iya kawo bala'i ko bacewar al'ada.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng