Kune makiyan damokradiya ba IGP ba - Sagay ga Majalisa

Kune makiyan damokradiya ba IGP ba - Sagay ga Majalisa

- Ciyaman kwamitin shawarwarin shugaban kasa game da rashawa (PACAC) Prof. Itse Sagay, ya bayyana cewa majalisa ta hanyar abubuwan da suke aikatawa sun nuna cewa sune matsalar damokradiyar Najeriya

- Majalisar ta bayyana IGP na ‘Yan Sanda a matsayin makiyin siyasa, inda tace bai cancanci rike wannan kujerar tasa ba

- Sagay yace IGP babu yanda za’ayi yaki amsa gayyatar da majalisar tayi masa saboda ya tura da wakili wanda kuma matsayin DIG gareshi amma majalisar taki amincewa ta saurare shi

Ciyaman kwamitin shawarwarin shugaban kasa game da rashawa (PACAC) Prof. Itse Sagay, ya bayyana cewa majalisa ta hanyar abubuwan da suke aikatawa sun nuna cewa sune matsalar siyasar Najeriya.

Majalisar ta bayyana IGP na ‘Yan Sanda a matsayin makiyin siyasa, inda tace bai cancanci rike wannan kujerar tasa ba.

Shugaban majalisar Bukola Saraki, ya bayyana haka a zaman majalisar na ranar Laraba, a babban birnin tarayya na kasa.

Kune makiyan damokradiya ba IGP ba - Sagay ga Majalisa

Kune makiyan damokradiya ba IGP ba - Sagay ga Majalisa

Sagay lokacin da yake zantawa da Daily Independent, yace IGP babu yanda za’ayi yaki amsa gayyatar da majalisar tayi masa saboda ya tura da wakili wanda kuma matsayin DIG gareshi amma majalisar taki amincewa ta saurare shi.

KU KARANTA KUMA: 'Yan ta'addan Houthi sun sake kai wa Saudiyya hari da makami mai linzami

Yace watsar da aikinsu da sukeyi don su ziyarci abokanan aikinsu wadanda ke fuskantar shari’a, ya nuna cewa sune makiya siyasa da cigaban Najeriya na asali.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel