Gwamna Gaidam ya amince da cire N63.5m don ciyarwa a watan Ramadan

Gwamna Gaidam ya amince da cire N63.5m don ciyarwa a watan Ramadan

- Gwamnan jihar Yobe Alhaji brahim Gaidam ya amince da bayar da N63.5m don ciyar da talakawa da kuma gudanar da Tafsiri a lokacin watan Ramadan

- Darakta janar na labarai da al’amuran gwamnan, Malam Abdullahi bego yace ciyarwar za’ayi ta ne a wurare 42 na kananan hukumomi 17 na jihar

- Bego yace a cikin kudin da gwamnan ya amince a fitar N48.5m za’ayi amfani dasu ne wurin sayen Raguna da kuma sarrafa kayan masarufi a wuraren 42 sannan kuma N15m za’ayi amfani dasu wurin biyan malaman tafsiri

Gwamnan jihar Yobe Alhaji brahim Gaidam ya amince da bayar da N63.5m don ciyar da talakawa da kuma gudanar da Tafsiri a lokacin watan Ramadan.

Darakta janar na labarai da al’amuran gwamnan, Malam Abdullahi bego yace ciyarwar za’ayi ta ne a wurare 42 na kananan hukumomi 17 na jihar.

Gwamna Gaidam ya amince da cire N63.5m don ciyarwa a watan Ramadan

Gwamna Gaidam ya amince da cire N63.5m don ciyarwa a watan Ramadan

Bego yace a cikin kudin da gwamnan ya amince a fitar N48.5m za’ayi amfani dasu ne wurin sayen Raguna da kuma sarrafa kayan masarufi a wuraren 42 sannan kuma N15m za’ayi amfani dasu wurin biyan malaman tafsiri na watan Azumin.

KU KARANTA KUMA: Dangote ya sake shiga jerin fitattun mutane 75 a duniya

“Gwamnan ya sake amince da bayar da buhunan shinkafa 1,260 sai jarkoki 630 na man gyada wadanda za’ayi amfani dasu a wuraren da za’a ringa raba abincin don a dafa abincin a wuraren 42 zauwa karshen watan Ramadan”, inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel