Rabin jihohin Najeriya basu iya tsayawa da kafafunsu, sabon rahoto

Rabin jihohin Najeriya basu iya tsayawa da kafafunsu, sabon rahoto

- Jihohin Arewa sunfi kowanne yanki talauci a Najeriya

- An bayyana jihohin da baza su iya tsayawa da kafarsu ba, koda Tarayya ta daina aiken kudi

- Wasu na ganin ko rushewa kasar nan tayi, wasu jihohin sai sun fi Nijar Talauci

Rabin jihohin Najeriya basu iya tsayawa da kafafunsu, sabon rahoto

Rabin jihohin Najeriya basu iya tsayawa da kafafunsu, sabon rahoto

A binciken da wata kungiyar tattalin arziki tayi, a 2017, batun bai canja ba ga jihohi 17 na kasar nan, kan yadda suke iya tara kudi daga haraji da ake yi a jiharsu.

Jihohin da abin ya shaa, sun kasa hada koda kashi 10 bisa dari na kudaden da Tarayya ke basu a duk wata daga arzikin kasa.

A kokarin da ake na iyar da jihohin kasar nan, na su tsaya da kafafunsu, yadda koda tarayyar ta tarwatse, ko kuma an daina samun kudin rabawa daidai, zasu iya zama da duwawunsu ba su ruguje ba.

DUBA WANNAN: Yadda rashin lafiyar shugaba Buhari zata canja 2019

Ogun, Rivers, Edo, Kwara, Enugu da Kano sune kawai suka iya tara N607 billion, in kaso talatin bisa dari, watau dai su sun ara kama hanyar tsira, kamar Legas.

Sauran kuwa N327 billion kawai suka iya tarawa kaf duk taronsu a bara 2017, wanda hakan na nuna babu wani aikin katabus da ake a jihohin.

Da yawan wandannan jihohi dai, basu da ko kamfani daya, wasunsu kuma basu da yawan masana'antun, sai dai da za'a dauki kidayar wuraren ibada na coci da masallatai, da sai aga ashe nan hankalin jama'ar yafi karkata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel