Ebola ta dawo Afirka: Cutar nan mai saurin kisa ta bullo a kasa mai yawan jama'a

Ebola ta dawo Afirka: Cutar nan mai saurin kisa ta bullo a kasa mai yawan jama'a

- Ebola bata da magani, kuma tana saurin yaduwa

- Ta kassara yammacin Afirka a 2014

- Ta sake bulla a kasar Kongo

Ebola ta dawo Afirka: Cutar nan mai saurin kisa ta bullo a kasa mai yawan jama'a

Ebola ta dawo Afirka: Cutar nan mai saurin kisa ta bullo a kasa mai yawan jama'a

Cutar Ebola, mai saurin yaduwa, mai kuma azabtarwa da kisa, ta bulla a kasar da aka fara gano ta shekaru 50 da suka wuce, watau kasar Congo.

Cutar dai bata jin magani, kuma ta kashe mutane da dama a kasashen yammacin Afirka bayan bullarta a Saliyo da Laberiya a baya.

A yanzu har ta kashe akalla mutum 17 a yankin mai yawan jama'a da hada-hada.

DUBA WANNAN: Kasar Amurka na son yaki ne, ko Israila ke ingiza ta?

Kasar Congo dai na makwabtaka da Kamaru, ita kuma Kamaru na makwabtaka ne da jihohin Borno, Adamawa, Taraba da Binuwai, sai kuma jihohin Kudu maso gabashin Najeriya.

Ana sa rai za'a shawo kan cutar kafin ta sha kan mutane, kamar yadda taso yi a baya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel