An kai sabon hari jihar Taraba, mutane 9 sun mutu

An kai sabon hari jihar Taraba, mutane 9 sun mutu

Hukumar 'yan sanda a jihar Taraba sun tabbatar da mutuwar mutane 9 a wani sabon hari da aka kai karamar hukumar Ussa dake jihar da safiyar yau, Laraba.

Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar, Asp David Misal, ya shaidawa manema labarai cewar, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai harin.

Misal ya ce tuni mataimakin kwamishinan 'yan sanda a jihar, Alhaji Aliyu Tafida, da ragowar wasu jami'an tsaro sun tafi garin domin ganewa idon su halin da garin ke ciki.

An kai sabon hari jihar Taraba, mutane 9 sun mutu

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku

Shugaban karamar hukumar Ussa, Mista Rimansikwe Karma, ya tabbatar da kai harin ga manema labarai tare da bayyana mutane uku sun samu raunuka.

A cewar Karma, maharan sun dira garin da misalin karfe 5:oo na safe yayin da jama'a ke fita domin yin ibada.

DUBA WANNAN: Fitacciyar 'yar siyasa ta shararawa 'yar jarida mari

"Duk ranar Laraba, jama'a kan fito a karshen dare domin gudanar da addu'o'in tsakiya mako. 'Yan bindigar sun kai harin ne a daidai lokacin da jama'a ke fitowa domin gudanar da addu'o'in tsakiyar wannan makon," a cewar Karma.

Karma ya kara da cewa, "Abin haushin shine maharan sun gudu kafin zuwan jami'an tsaro. Mutane 9 ne suka mutu yayin mutane uku da suka samu rauni ke samun kulawa a babban asibitin garin Takum."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel