Gwamnati na shirin kashe Biliyan N30b don magance Kashi da Fitsari a wajen banɗaki

Gwamnati na shirin kashe Biliyan N30b don magance Kashi da Fitsari a wajen banɗaki

- Gwamnatin Buhari za tayi maganin masu kwaye zani da cire wando suna tsuguno akan titi

- Shirin dai za'a aiwatar da shi ne a karkashin Ma'aikatar ruwa da tsaftar muhalli

Dabi’ar Fitsari ko kashi a kan titi ta zama ruwan dare, kuma tana haddasa cututtuka baya ga shubar da mutunci da kima, Gwamnatin Buhari na shirin magance wannan mummunan halayya.

Gwamnati na shirin kashe Biliyan N30b don magance Kashi da Fitsari a wajen banɗaki

Gwamnati na shirin kashe Biliyan N30b don magance Kashi da Fitsari a wajen banɗaki

Babban Darakta a ma’aikatar ruwa da tsaftar muhalli Mr Emmanuel Awe na ma’aikatar albarkatun ruwa ta kasa ya ce, ma’aikatarsu ta ne gwamnati da ta bata Naira biliyan N30b domin ta magance mummunar dabi’ar nan ta yin kasha da fitsari a bainar jama’a a fadin kasar nan.

Babban Daaraktan ya fadi hakan ne yau a Abuja yayin da ya karbi bakuncin hadakar kungiyar kula da wadatar ruwa da tsaftar muhalli (Wncin SSCC) karkashin jagorancin babban Daraktanta Mr Rolf Luyendijk.

KU KARANTA: Karfin hali: ‘Yan Najeriya 17 da suka tsallake nitsewa cikin kogi sun kai kasar Italiya kara (Hotuna)

Babban Daaraktan ya fadi hakan ne yau a Abuja yayin da ya karbi bakuncin hadakar kungiyar kula da wadatar ruwa da tsaftar muhalli (Wncin SSCC) karkashin jagorancin babban Daraktanta Mr Rolf Luyendijk.

Gwamnati na shirin kashe Biliyan N30b don magance Kashi da Fitsari a wajen banɗaki

Gwamnati na shirin kashe Biliyan N30b don magance Kashi da Fitsari a wajen banɗaki

A cewar Mr. Awe ya kamata gwamnatocin jahohi su fara ware kudade domin tabbatar da tsaftar muhalli. Domin hakan ya zama wajibi mutukar ana son magance dabi’ar yin fitsari ko ba haya a waje da yanzu ya zama ruwan dare.

Wannan ne dalilin da ya sanya a cikin kasafin 2018 muka ware kudaden tsaftar ruwan sha da ta muhalli, kuma lallai ya kamata a cigaba da wayar da kan gwamnatoci a matakai daban-daban don su rungumi tsarin.

A nasa jawabin Luyendijk cewa yayi, wadatuwar tsaftataccen ruwan sha wata alama ce dake nuna kasa bata cikin matsanancin talauci. A sakamakon haka me yayi kira da mayar da hankali sosai wajen bullo da shirye-shirye da zasu habaka rayuwar Mutane baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel