Zaben 2019: PDP na tunanin tsayar da Atiku

Zaben 2019: PDP na tunanin tsayar da Atiku

- PDP na cigaba da shirye-shiryen karbar mulki daga hannun APC a 2019

- Sun shirya tsayar da dan takarar da zai kara da Muhammadu Buhari

- Zasu tsayar da shugaban da zai samarwa da Matasan Najeriya aiki

Yayin da kakar zabe ke kara gabatowa, jam’iyyar PDP a yunkurinta na lalubu dan takarar da zai karbu a Arewaci da kuma kudancin Najeriya, na tunanin tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin wanda zai kara da ‘yan takarar sauran jam’iyyu domin darewa kan karagar mulkin kasar nan a 2019.

Zaben 2019: PDP na tunanin tsayar da Atiku

Atiku Abubakar- Tsohon Mataimakin shugaban Kasa

Wanan Magana dai na fitowa ne daga bakin wani jigo a jam’iyyar da ya bukaci a boye sunansa a wata hira da jaridar Vanguard yau Laraba.

KU KARANTA: Jami’an ‘Yan Sanda sun ceci Shugaban Jam’iyyar APC a Ekiti

A cewarsa, jam’iyyar tasu na sane da irin wuyar da kayar da gwamnati mai ci ke da shi, wannan ne ma dalilin da yasa suke son fitowa da dan takarar da zai karbu cikin sauki.

Domin Najeriyar da da ta yanzu ba daya ba ce, yanzu muna maganar samawa mutane aikin yi ne, kuma kowa yasan yadda Atiku yayi kokari a wannan fannin.” Majiyar ta nanata.

Daga nan ne kuma boyayyiyar majiyar ta bayyana cewa kofa a bude take ga duk wanda yake son dawowa cikin jam’iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel