‘Yar Siyasa ta sheke ‘yar jarida da mari saboda tayi kokarin daukar hoton ta

‘Yar Siyasa ta sheke ‘yar jarida da mari saboda tayi kokarin daukar hoton ta

A kasar Ghana, kafofin yada labarai sun rawaito cewar wata ‘yar siyasa, mamba a jam’iyya mai mulki, ta sheke wata ‘yar jarida da mari tare da bayyana cewar ‘yar jaridar tayi kama da masu sayar da albasa.

CitiNews dake kasar Ghana ta rawaito cewar, ‘yar siyasar, Hajiya fati, kusa a jam’iyyar NNP mai mulki ta mari ‘yar jaridar ne saboda ta so daukan hoton ta a satin day a gabata.

Da take kare kan ta, Hajiya Fati, ta bayyana cewar, “nayi zaton tana daga cikin mutanen Mista Sammy Crabbe, ‘yan jam’iyyar adawa, domin kwata-kwata bata yi kama da ‘yan jarida ba.” Mutane da dama basu amince da wannan hujja ta Hajiya Fati ba.

‘Yar Siyasa ta sheke ‘yar jarida da mari saboda tayi kokarin daukar hoton ta

‘Yar Siyasa, Hajiya Fati

Wani jigo a gidauniyar kula da masu aikin jarida a Afrika ta yamma, Sulemana Braimah, ya bayyana shakku a kan kare hakkin ‘yan jarida a ofishin jam’iyyar NPP mai mulki a kasar Ghana.

DUBA WANNAN: Jirgin zanga-zangar neman sakin Sheikh El-Zakzaky ya dira a jihar Legas

Kazalika kungiyar ‘yan jarida a kasar Ghana ta bayyana cewar mai yiwuwa ta shigar da kara kotu domin nemawa ‘yar jaridar hakkin ta a wurin ‘yar siyasar.

Saud a dama ‘yan jarida kan shiga halin tsaka mai wuya ko fuskantar cin mutunci yayin gudanar da aiyukan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel