Hukumar ICPC zata gurfanar da darektan hukumar SEC, Gwarzo, da aka dakatar

Hukumar ICPC zata gurfanar da darektan hukumar SEC, Gwarzo, da aka dakatar

- Hukumar yaki da rashawa na ICPC ta gurfanar da daraktan hukumar SEC, Mounir Gwarzo

- Ana tuhumarsa ne da karabar naira miliyan 104 a matsayin kudin sallama duk da cewa bai ajiye aiki ba

Hukumar binciken masu aikata rashawa ICPC ta gurfanar da daraktan Hukumar kula da hada-hadan hannun jari (SEC), Mounir Gwarzo a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja kotu bisa zarginsa da laifin damfara.

Ministan kudi, Kemi Adesosun ne ta dakatar da Gwarzo a watan Disambar bara saboda zarginsa da aikata damfara.

Hukumar ICPC zata gurfanar da darektan hukumar SEC, Gwarzo, da aka dakatar

Hukumar ICPC zata gurfanar da darektan hukumar SEC, Gwarzo, da aka dakatar

KU KARANTA: Ana mutunta Najeriya a duniya ne saboda Buhari

An dakatar dashi ne tare da wasu manyan jami'an hukumar guda biyu; Abdulsalam Habu, shugaban hulda da kafafen yada labarai da kuma Anastasia Braimoh, shugaban sashin shari'ah.

Jaridar Premium Times ta gano cewa an dakatar da Mr Gwarzo ne a daidai lokacin da ya bayar da umurnin a gudanar da binciken hada-hadan kudade da kamfanin man fetir na Oando ke gudanarwa.

A halin yanzu kuma, Punch ta ruwaito cewa an gurfanar da Mr. Gwarzo tare da wasu mukarabbansa a ranar Laraba. Ana tuhumar sa da karabar cin hanci na naira miliyan 104 a matsayin kudin sallama cikin kafin wata daya da fara aikinsa.

Sai dai kakakin hukumar ta ICPC, Rasheedat Okoduwa ta ce ba za tayi tsokaci a kan labarin gurfanar da Gwarzo a kotu ba saboda ba'a sanar da ita a 'hukumance' ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel