IGP Idris makiyin Demokradiyya ne kuma za mu dau mataki a kanshi – Majalisan Dattawa bayan ganawar sirri

IGP Idris makiyin Demokradiyya ne kuma za mu dau mataki a kanshi – Majalisan Dattawa bayan ganawar sirri

Majalisan dattawan Najeriya ta alanta sifeto janar na hukumar yan sanda, Ibrahim Idris, a matsayin makiyin demokradiyya wanda bai cancanci rike mukamin gwamnati ba.

Shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana hakan ne bayan ganawar sirri da sukayi a yau Laraba.

Sanatocin Najeriya sun shiga wata ganawa ta sirri domin daukan mataki a kan babban Sifeton sanadiyar rashin bayyanarsa gabansu karo na uku a jere.

Ganawar da suka far tun karfe 12:24 na rana ya kwashi mintuna 50.

Bayan ganawar, Sanata Bukola Saraki yace: “Majalisa ta siffanta wannan rashin bayyana gabanta a matsayin hadari ga demokradiyyamu kuma saboda haka, majalisan dattawa ta alanta IGP a matsayin makiyin demokradiyya….. Shugaban masu runjaye yayi dubi cikin wannan al’amari domin sauran matakai.”

IGP Idris makiyin Demokradiyya ne kuma zamu dau mataki a kanshi – Majalisan Dattawa bayan ganawar sirri

IGP Idris makiyin Demokradiyya ne kuma zamu dau mataki a kanshi – Majalisan Dattawa bayan ganawar sirri

Za ku tuna mun kawo muku rahoton cewa a karo na uku, sifeton hukumar yan sandan Najeriya, IGP Ibrahim Idris, ya ki bayyana gaban majalisan dattawan Najeriya a yau Laraba, 9 ga watan Mayu, 2018.

KU KARANTA: Majalisar dattijai zata dauki tsatstsauran mataki a kan Sifeton 'yan sanda, sun shiga ganawar sirri

Majalisan dattawan Najeriya sun gayyaci sau uku kenan domin ya amsa tambayoyi akan yadda hukumar yan sanda suke cin mutuncin Sanata Dino Melaye da ake zargi da daukan nauyin masu garkuwa da mutane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel