Ana dakon manyan jirage guda 32 dauke da man fetir da kayayyakin abinci zuwa Najeriya

Ana dakon manyan jirage guda 32 dauke da man fetir da kayayyakin abinci zuwa Najeriya

Kimanin jiragen dankaro dai dai har guda 32 ne suke tafe aka hanyarsu ta zuwa Najeriya, ta jihar Legas daga sassa daban daban na kasashen Duniya, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Jiragen suna dauke ne da tataccen man fetir gami da kayan abinci daban daban, kuma ana sa ran zasu iso tashoshin jiragen ruwa dake jihar Legas, tashar Apapa da Tin Can Island, tun daga ranar 9 ga watan Mayu zuwa 26 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Mutane 3 Uku sun mutu a wani tashin tashin da ya wakana a jihar Nassarawa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa na Najeriya, NPA ce ta sanar da tasowar jiragen, inda tace guda 9 daga cikin 32 na dauke ne da tataccen man fetir.

Ana dakon manyan jirage guda 32 dauke da man fetir da kayayyakin abinci zuwa Najeriya

Jirgin dankaro

Hukumar NPA ta kara da cewa sauran jirage 23 na dauke ne da acca, kifi, sundukai, taki tare da sauran nau’o’in kayayyaki daban daban. Daga karshe hukumar ta ce zuwa yanzu jirage dake dauke da taki, siga, kifi, man jirgin sama da man fetir sun iso jihar Legas.

Already, eight ships have arrived the ports waiting to berth with bulk fertiliser, sugar, frozen fish, aviation fuel and petrol. (NAN)

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel