Yanzu-yanzu: Karo na uku, IGP Idris ya yi fatali da gayyatan majalisar dattawa

Yanzu-yanzu: Karo na uku, IGP Idris ya yi fatali da gayyatan majalisar dattawa

A karo na uku, sifeton hukumar yan sandan Najeriya, IGP Ibrahim Idris, ya ki bayyana gaban majalisan dattawan Najeriya a yau Laraba, 9 ga watan Mayu, 2018.

Majalisan dattawan Najeriya sun gayyaci sau uku kenan domin ya amsa tambayoyi akan yadda hukumar yan sanda suke cin mutuncin Sanata Dino Melaye da ake zargi da daukan nauyin masu garkuwa da mutane.

Majalisan ta fara gayyatansa ne ya bayyana ranan 25 ga watan Afrilu, 2018 amma ya ki. Ya laburta shugaban kwamitin harkokin yan sanda a majalisar dattawa, Abu Ibrahim, cewa zai raka shugaba Muhammadu Buhari jihar Bauchi.

Yanzu-yanzu: Karo na uku, IGP Idris ya yi fatali da gayyatan majalisar dattawa

Yanzu-yanzu: Karo na uku, IGP Idris ya yi fatali da gayyatan majalisar dattawa

Sanata Abu Ibrahim ya ce a makon da ya gabata ya yi kokarin tuntuban sifeton amma bai same shi ba. Daga baya sai ya samu labarin cewa ya tafi jihar Kaduna a maimakon zuwa majalisa.

KU KARANTA: Kashin kadangare matasa ke zuka yanzu don maye – Likitan mahaukata, Taiwo Sheikh

Bisa ga shawaran shugaban majalisa, Bukola Saraki, an sake gayyatarsa ya bayyana yau amma ya sake watsa musu kasa a ido.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel