Ka ji tausayinmu ka ceto mu - Ma’aikatan asibiti 3 da Boko Haram suka sace sun rubuta wasika ga shugaba Buhari

Ka ji tausayinmu ka ceto mu - Ma’aikatan asibiti 3 da Boko Haram suka sace sun rubuta wasika ga shugaba Buhari

Ma’aikaciyar asibiti ‘Nurse’ daya da masu agazawa masu ciki 2 da Boko Haram sukayi garkuwa da su ranan 1 ga watan Maris, 2018 sun rubuta wasika ga shugaba Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima.

Ma’aikatan - Mrs. Alice Loksha Ngaddah, Hauwa Mohammed Liman da Saifura Husseini Ahmed – sun ce suna cikin halin kunci kuma suna son komawa wajen iyalensu.

Wasikar yace: “ Ga shugabannin kungiyoyinmu, ku ji tausayinmu. Ku ceto mu, iyalanmu na bukatanmu da kuma kasa ga baki daya,”.

Ka ji tausayinmu ka ceto mu - Ma’aikatan asibiti 3 da Boko Haram suka sace sun rubuta wasika ga shugaba Buhari

Ka ji tausayinmu ka ceto mu - Ma’aikatan asibiti 3 da Boko Haram suka sace sun rubuta wasika ga shugaba Buhari

Wadannan mata sun kasance suna aiki karkashin kungiyar International Committee of Red Cross (ICRC)/ United Nation Children Education Fund (UNICEF) yayinda akayi garkuwa da su ranan Alhamis, 1 ga watan Maris a Kala-Balge, karamar hukumar Rann a jihar Borno.

KU KARANTA: Kashin kadangare matasa ke zuka yanzu don maye – Likitan mahaukata, Taiwo Sheikh

Jaridar Sahara Reporters da bada wannan rahoto ta ce shahrarren da jaridan nan, Ahmad Salkida, ne ya samo wasikar da matan suka rubuta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel