Gwamnatin Tarayya ta malalo N3trn domin ci gaban gine-gine a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta malalo N3trn domin ci gaban gine-gine a Najeriya

Mun samu rahoton cewa gwamnatin tarayya ta ware sama da naira tiriliyan 3 domin samar da ci gaban gine-gine a fadin kasar nan.

Karamin ministan makamashi, aiki da gidaje, Suleiman Zarma, shine ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata yayin ziyarar gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, ministan tare da tawagar sa ta wasu jiga-jigan ma'aikatar sa sun ziyarci jihar ne a wani bangare na ci gaba da tantance aikace-aikace gwamnatin tarayya na tituna, gidaje da kuma makamashi.

Gwamnatin Tarayya ta malalo N3trn domin ci gaban gine-gine a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta malalo N3trn domin ci gaban gine-gine a Najeriya

Ministan ya bayyana cewa, babbar manufa ta wannan shawagi da gewaye da suke aiwatar shin tabbatar da nasarorin da gwamnatin tarayyar kasar nan ta dukufa wajen samarwa sabanin yadda ake kushe hobbosa da jajircewar ta.

KARANTA KUMA: Cutar Ebola ta sake bayyana a jamhuriyyar Congo, rayuka 17 sun salwanta

Legit.ng ta fahimci cewa, ministan ya kuma bayyana yadda gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ke cika alkawurran ta na kawo ci gaban gine-gine a kasar nan.

A yayin haka ministan ya kara da cewa, kawowa yanzu gwamnatin ta batar da sama da N3trn wajen samar da ci gaba ta fuskar gine-gine wanda za a samu doriya kan wannan adadin cikin kasafin kudi mai gabatowa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel