Gwamnatin Buhari za ta kawo karshen ruwa-ruwan ‘Daliban da ake yayewa a Jami’o’i

Gwamnatin Buhari za ta kawo karshen ruwa-ruwan ‘Daliban da ake yayewa a Jami’o’i

Mun ji cewa Gwamnatin Shugaban kasa Buhari na shirin kawo wani tsarin ilmi da zai sa a maida wadanda su ka kammala karatu a Jami’a zuwa wasu makarantu na musamman a kasar domin kara kwarewa idan har an yarda.

Karamin Ministan ilmi na Najeriya Farfesa Anthony Anwukah ya kawo wani tsarin da zai sa wadanda su ka gama karatu su kara sanin makamashin aiki a kasar. Ministan ya bayyana wannan ne a wajen wani taron Jami’o’i.

Gwamnatin Buhari za ta kawo karshen ruwa-ruwan ‘Daliban da ake yayewa a Jami’o’i

Ministan ilmi yace yana so a fara koyawa ‘Yan makaranta aiki

Hukumar NUC da ke kula da Jami’o’in kasar nan ta shirya wani taro kwanaki inda Farfesa Anwukah ya bayyana cewa ya kamata a rika horar da sauran wadanda su kayi karatu a Jami’a kamar yadda ake yi wa Likitoci da kuma Alkalai.

Alkalai da Malaman asibiti kan tsaya su koyi aiki na shekara guda kafin su fara aiki a kasar don haka ne Ministan ilmin yake cewa za a rika horar da wadanda su ka karanta wasu kwas din a Jami’a domin su kware yadda ya kamata.

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun gano wata kasuwar makamai a Najeriya

Ana dai kokarin ganin ana yaye ‘Daliban da su ka san bakin zaren aiki a kasar. Farfesa Anwuka yace tsarin SIWES da aka kafa a da domin koyawa ‘Yan makaranta aiki bai bada wata fa’ida ba don haka ake neman kawo gyara yanzu.

Idan abin ya yiwu za a rika amfani da Makarantar koyon kasuwanci da ke Legas domin horar da wadanda su ka karanci kasuwanci da tattali da kuma irin su Kwalejin NTA da ke Jos domin horar da ‘Yan Jarida inji Ministan kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel