Ana musayar kalamai tsakanin ministan Buhari da gwamna Ajimobi

Ana musayar kalamai tsakanin ministan Buhari da gwamna Ajimobi

A jiya ne ministan sadarwa na kasa, Adebayo Shittu ya yi ikirarin cewa gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo yana tsoron sa. Ya ce Ajimobi na tsoron zuwa gidan yari saboda ya san cewa yayi almubazaranci da kudaden jihar kuma mudin Shittu ya zama gwamna zai bankado abubuwan da ya yi.

Shi kuma gwamna Ajimobi ya kada baki ya ce ministan ya kamata ya rika fargaban zuwa gidan yari saboda tuhume-tuhumen da ake masa.

A yayin da Shittu ya ke zantawa da manema labarai lokacin da ya kai ziyara Sakateriyar APC da ke Abuja, ya shaida musu cewa gwamna Ajimobi yana fargabar cewa idan Barrister ya maye gurbinsa a matsayin gwamna, tabbas sai ya tafi kurkuku.

Ana musayar kalamai tsakanin ministan Buhari da gwamna Ajimobi

Ana musayar kalamai tsakanin ministan Buhari da gwamna Ajimobi

KU KARANTA: Kungiyar musulmi ta JNI ta baiwa gwamnati wata shawara game da haramta kodin

"A ganinsa bani tankwasuwa a duk wani lamari da ya shafi biyaya ga doka da sanin ya kamata. Hakan yasa ya ke kokarin ganin tsohe duk wata kafa da zata bani daman zama gwamna." inji Shittu.

Ministan ya cigaba da cewa a matsayinsa na Lauya wanda ya yi imani da doka, zai yi takaran fida gwani ba tare da kunbiya-kunbiya ba kuma idan baiyi nasara ba zai koma yayi wani abu daban da rayuwarsa.

Da aka masa tambaye ko kwamitin sulhu na jam'iyyar APC da Tinubu ke jagoranta ya nemi sulhunta shi da gwamnan amma Ministan ya ce babu wanda ya tuntube shi game da maganar sulhu a halin yanzu.

An dai dade ba'a ga maciji tsakanin gwaman Ajimobi da Ministan sadarwa Shittu a boye da kuma bainar mutane har ma da kafafen yadda labarai.

Sai dai wata sanarwa da ta fito daga bakin hadimin gwamna Ajimobi, Mr. Bolaji Tunji ya ce ministan ne ya kamata yayi fargaban zuwa gidan yari saboda irin tuhume-tuhumen da wasu hadimansa da suka ajiye aiki suke masa akan rashin biyansu hakokinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel