Kungiyar musulmi ta JNI ta baiwa gwamnati wata shawara game da haramta kodin

Kungiyar musulmi ta JNI ta baiwa gwamnati wata shawara game da haramta kodin

- Kungiyar JNI ta shawarci gwamnatin tarayya ka kafa doka da zai karfafa haramta amfani da kodin

- Kungiyar ta tayi na'am ta haramta kodin din inda tace galibin matasan arewa suna shaye-shayen miyagun kwayoyi

- Kungiyar kuma tayi kira da malamai suyi amfani da damar da zasu samu a watan Ramadhan wajen fadakar da mutane sharrin shan miyagun kwayoyi da kalaman kiyaya

Bayan haramta hadawa da siyar da magunguna masu dauke da sinadarin kodin da gwamnatin tarayya tayi cikin kwanakin nan, kungiyar musulunci na Jama'atul Nasril Islam (JNI) ta yi kira da gwamnatin tarayya ta kafa dokoki da zasu fayyace hukuncin wanda ya saba umurnin.

Sakatare Janar na JNI, Khalid Aliyu, ne yayi wannan kirar a ranar Talata yayin da yake hira da manema labarai bayan wani taron da kungiyar ta saba yi kafin Ramadhan a Kaduna.

Kungiyar musulunci ta JNI tayi tsokaci kan haramta kodin da gwamnati tayi

Kungiyar musulunci ta JNI tayi tsokaci kan haramta kodin da gwamnati tayi

"Muna godiya ga Allah cewa gwamnatin tarayya ta haramta amfani da kodin, amma ya dace akwai rubutacciyar doka da zata fayyace irin hukuncin da za'ayi wa wadanda aka samu suna cigaba da safarar kodin din."

Mr. Aliyu ya ce shaye-shayen miyagun kwayoyi matsala ne da ya dade yana adabar matasan arewa musamman yadda galibin su ke shan kodin da wasu magungunan tarin makamanta hakan.

Yayi kira da sauran malamai suyi amfani da damar da zasu samu a watan Ramadhan don su cigaba da fadakar da al'umma kan sharrin da ke tattare da ta'amulli da miyagun kwayoyi.

Ya kuma yi kira ga malamai su kauracewa fadawa cikin harkokin siyasa a yayin da suke wa'azin su kuma su fadakar da mutane ilolin kalaman nuna kiyaya da batanci.

Gwamnatin tarayyan dai ta haramta amfani da duk wani magani mai dauke da kodin ne a rana 1 ga watan Mayun 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel