Harin Majalisa: Omo-Agege zai riski dakatarwa ta har abada

Harin Majalisa: Omo-Agege zai riski dakatarwa ta har abada

- Bayan satuttuka da ‘yan ta’adda suka shiga majalisa suka sace sandar girma, wadda itace shaidar doka, alamu sun bayyana cewa shugabannin majalisa na shawarar sake dakatar da sanata Ovie Omo-Agege

- Hakan yazo ne bayan kusan sa’o’I 24 da shugaban majalisar Bukola Saraki, ya gana da shugaba Muhammadu Buhari akan lamarin ta’addancin da aka yiwa majalisar

- Omo-Agege an dakatar dashi ne sati daya kafin shigar da akayi majalisar akayi mata ta’addancin satar sandar girma wanda ake zarginsa da yiwa ‘yan ta’addan jagora zuwa cikin majalisar

Bayan satuttuka da ‘yan ta’adda suka shiga majalisa suka sace sandar girma, wadda itace shaidar doka, alamu sun bayyana cewa shugabannin majalisa na shawarar sake dakatar da sanata Ovie Omo-Agege.

Hakan yazo ne bayan kusan sa’o’I 24 da shugaban majalisar Bukola Saraki, ya gana da shugaba Muhammadu Buhari akan lamarin ta’addancin da aka yiwa majalisar da kuma wasu lamurran da suka shafi majalisar.

Omo-Agege an dakatar dashi ne sati daya kafin shigar da akayi majalisar akayi mata ta’addancin satar sandar girma wanda ake zarginsa da yiwa ‘yan ta’addan jagora zuwa cikin majalisar, duk da cewa a gardanta hakan.

Harin Majalisa: Omo-Agege zai riski dakatarwa ta har abada

Harin Majalisa: Omo-Agege zai riski dakatarwa ta har abada
Source: Depositphotos

‘Yan ta’addan sun shiga majalisar ne a ranar 18 ga watan Afirilu, lokacin da majalisar ke cikin zamanta na tattaunawa game da lamurran da suka shafi kasa.

Bayan aukuwar lamarin shuwagabannin majalisar sun kafa kwamitin binciken aukuwar lamarin a ranar 25 ga watan Afirilu, wanda mataimakin shugaban majalisar Bala ibn Na’Allah aka bashi sati biyu don ya bayar da rahoto ga majalisar don daukar matakin da ya dace.

KU KARANTA KUMA: Masu kula da shugaba Buhari na boye rashin lafiyarsa – PDP

Shugaban majalisa Bukola Saraki a jiya ya bayyana cewa an gama bincike bayan rahoton da kwamitin kula da korafin jama’a ya bayar wanda Samuel Anyanwu ya jagoranta, sakamakon haka cikin matakan da majalisar zata iya dauka sun hada da sake dakatar da Omo-Agege.

Idan dai bazaku manta ba a kwanakin baya ne wasu yan daba suga shiga zauren majalisa a lokacin da ake zama inda suka dauke sandar iko na majalisar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel