Dalili daya 1 da yasa Yarbawa ba su zabe ni ba a 1999 - Obasanjo

Dalili daya 1 da yasa Yarbawa ba su zabe ni ba a 1999 - Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya kuma na farko a wannan jamhuriyar Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilin da yake tunanin shine ya sanya 'yan kabilar yarbawa basu zabe sa ba a zaben 1999.

A cewar Cif Obasanjo, yana tunanin saboda ya ki ya shiga kungiyar nan ta hadaddiyar kabilar yarbawan dake kare muradun su ta Afenifere da Marigayi Sanata Abraham Adesanya yake shugabanta a wancan lokacin ne ya janyo hakan.

Dalilin daya 1 da yasa Yarbawa ba su zabe ni ba a 1999 - Obasanjo

Dalilin daya 1 da yasa Yarbawa ba su zabe ni ba a 1999 - Obasanjo

Legit.ng ta samu cewa Cif Obasanjo ya ayyana hakan ne a lokacin da yake jawabin sa a lokacin taron shekaru 10 na tunawa da Sanata Abrahim din a birnin Legas.

A wani labarin kuma, Uwar gidan tsohon shugaban kasar Najeriya Patience Jonathan ta kara shiga wata tsomomuwar biyo bayan umurnin wata babbar kotu dake zaman ta a garin Legas na kwace zunzurutun kudaden ta da suka kai Naira 9.2 biliyan, Dala 8.4 miliyan ta kuma ba gwamnatin tarayya.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu ta ce a baya ne dai hukumar nan dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ne suka kai ta kara.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel