Masu kula da shugaba Buhari na boye rashin lafiyarsa – PDP

Masu kula da shugaba Buhari na boye rashin lafiyarsa – PDP

- Jam’iyyar PDP tace masu kula da shugaba Muhammadu Buhari sun zabi su boye lamarin rashin lafiyarsa wadda taki karewa

- Jam’iyyar tace ‘yan Najeriya bai zama lallai a sanar dasu yanayin rashin lafiyar shugaban kasar ba da kuma wanene Likitansa na kasar Ingila ba saboda matsala ne ga siyasar Najeriya

- Sakataren tarayya na jam’iyyar PDP Kola Ologbondiya, ya bayyana cewa jam’iyyar tasu ba wai bata goyon bayan shugaban kasar ya kula da lafiyarsa bane, amma dai a san gaskiyar minene ke damunsa

Jam’iyyar PDP tace masu kula da shugaba Muhammadu Buhari sun zabi su boye lamarin rashin lafiyarsa wadda takici taki cinyewa.

Jam’iyyar tace ‘yan Najeriya bai zama lallai a sanar dasu yanayin rashin lafiyar shugaban kasar ba da kuma wanene Likitansa na kasar Ingila ba saboda matsala ne ga siyasar Najeriya.

Sakataren tarayya na jam’iyyar PDP Kola Ologbondiya, a ranar Talata a birnin tarayya, ya bayyana cewa jam’iyyar tasu ba wai bata goyon bayan shugaban kasar ya kula da lafiyarsa bane, amma dai a san gaskiyar minene ke damunsa.

KU KARANTA KUMA: Ina tsoron mutuwar Zakzaky a hannun gwamnati - Campbell

Sun kara da cewa ya kamata a sanar da ‘yan Najeriya abunda ke damun shugaban kasar da kuma wanene likitansa sannan a wane asibiti ne ake dubashi, tinda sunce wannan gwamnati ce wadda bata boye komai.

A jiya ne dai shugaban kasa Buhari ya bar kasar inda ya sanar da cewa zai dauki tsawon kwanaki hudu domin ganin likitansa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel