Akwai ha’inci: Minista Fashola ya fadawa ‘Yan kwangila su shirya sabon aiki

Akwai ha’inci: Minista Fashola ya fadawa ‘Yan kwangila su shirya sabon aiki

- Gwamnatin Tarayya ba ta amince da nagartar wasu ayyuka da aka yi ba

- Ministan ayyuka ya nemi a gyara wasu gine-gine da aka yi a Jihar Kebbi

- Fashola ya bada umarni ayi maza a sake wadannan ayyuka tun da wuri

Mun samu labari daga Jaridun kasar nan cewa Ministan ayyuka Babatunde Fashola ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba za tayi na’am da wasu gidaje da ‘Yan kwangila su ka gina a Jihar Kebbi ba inda aka nemi a gyara ginin.

Akwai ha’inci: Minista Fashola ya fadawa ‘Yan kwangila su shirya sabon aiki

Ministan ayyuka bai yadda da wasu kwangiloli da aka yi ba

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta nemi ‘Yan kwangila su sake sabon aikin gidaje 74 da aka gina da kuma titi da aka yi a Birnin Kebbi da kuma hanyar Jega zuwa Yauri. Minista Fashola yace ‘yan kwangilar sun yi aika-aika.

Gwamnatin Tarayya ba ta amince da nagartar wadannan ayyuka da aka yi ba kamar tadda Ministan ayyuka na kasar ya nuna. Raji Fashola yace an yi ha’inci wajen rufin da aka yi wa gidajen da aka gina da kuma dandamalin da aka yi.

KU KARANTA: Babu tabbacin ranar dawowar Shugaba Buhari Najeriya

Ministan yace an ba masu aikin kudin su don haka dole yanzu su cika alkawarin da aka yi da su. Shugaban Kamfanin na TRIACTA da aka ba wannan aiki Walid Abou Joude yace za su yi bakin kokarin su na gyara aikin cikin gaggawa.

An dai kammala wani sashen na aikin titin na tsawon kilomita 186 wanda ya tashi tsakanin Jega da Yauri zuwa Garin Sokoto. Aikin wannan dogon titi dai zai kai har cikin Garin Birnin-Kebbi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel