Babbar magana: Yan sandan Najeriya sun gano kasuwar bindigogi a Arewa

Babbar magana: Yan sandan Najeriya sun gano kasuwar bindigogi a Arewa

Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Benue dake a yankin Arewa ta tsakiya sun ayyana samun nasarar cafke wasu mutane da suka ce suna gudanar da kasuwancin saye da sayarwar muggan makamai.

Kamar dai yadda muka samu, a ranar Talatar da ta gabata ne dai rundunar ta 'yan sanda ta gabatar da wadanda take zargi da aikata laifin ga 'yan jarida a harabar hedikwatar 'yan sandan dake a garin Makurdi.

Babbar magana: Yan sandan Najeriya sun gano kasuwar bindigogi a Arewa

Babbar magana: Yan sandan Najeriya sun gano kasuwar bindigogi a Arewa

KU KARANTA: An ba hamata iska tsakanin sojoji da jami'an NSCDC

Legit.ng ta samu cewa haka zalika 'yan sandan kuma sun sha alwashin cigaba da aiki tukuru domin ganin sun ga bayan ayyukan ta'addanci da kashe-kashen da yanzu haka suka yi kamari a jihar da makwaftan ta.

A wani labarin kuma, Uwar gidan tsohon shugaban kasar Najeriya Patience Jonathan ta kara shiga wata tsomomuwar biyo bayan umurnin wata babbar kotu dake zaman ta a garin Legas na kwace zunzurutun kudaden ta da suka kai Naira 9.2 biliyan, Dala 8.4 miliyan ta kuma ba gwamnatin tarayya.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu ta ce a baya ne dai hukumar nan dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ne suka kai ta kara.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel