An tashi baram baram a wani taron sulhu tsakanin yan takarakarun Gwamna a jam’iyyar APC

An tashi baram baram a wani taron sulhu tsakanin yan takarakarun Gwamna a jam’iyyar APC

Ministan tama da karafa, Kayode Fayemi ya fice daga taron sulhu a tsakanin yan takarkarun kujerar gwamnan jihar Ekiti a karkashin jam’iyyar APC, wanda jagoran APC, Ahmed Bola Tinubu ya shirya, inji rahoton jaridar ‘The Cable.’

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan taro ya gudana ne a ranar Talata 8 ga watan Mayu a gidan gwamnatin jihar Legas dake babban birnin tarayya Abuja, kuma ya samu halartar jigogin APC da suka hada da tsohon shugaban APC, Bisi Akande, Segun Osoba, Niyi Adebayo da Pius Akinyelure.

KU KARANTA: Turnuku: An kwashi yan kallo a wani hari da Sojoji suka kai ma Yansanda a Legas

Bayan tattaunawa na tsawon awanni biyu ne, sai aka tsagaita na wasu yan mintoci, a wannan nan lokaci ne ministan ya fice daga taron, tare da yin watsi da jigon APC, Ahmed Bola Tinubu, inda ya shige motarsa, ya yi tafiyarsa.

An tashi baram baram a wani taron sulhu tsakanin yan takarakarun Gwamna a jam’iyyar APC

Fayemi

Sai dai bayan kammala taron, Akande ya bayyana ma yan jaridu cewa zasu mika ma uwar jam’yya shawarwarin da suka dauka a taron, don haka yace sun dauki matakan da zasu dadada ma jam’iyyarsu, da ma yan takarkarun gaba daya.

Bugu da kari da aka sake tambayarsa game da ko jam’iyyar zata fidda dna takara na yarjejeniya, sai yace ai kundin tsarin mulki bai hana ba, kuma sun bukaci Yan takarkarun da su je su yi tunani game da hakan, kuma su kawo musu amsoshinsu.

An tashi baram baram a wani taron sulhu tsakanin yan takarakarun Gwamna a jam’iyyar APC

Tinubu da Akande bayan taron

Idan za’a tuna, a satin data wuce ne aka samu hatsaniya a zaben cikin gida na zaben dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC, inda wasu yan bangan siyasa suka dira wajen zaben, suka tayar da tarzoma. Sai dai wasu na zargin Minista Fayemi ne ya aiko yan bangan siyasar.

Zuwa yanzu dai uwar jam’iyyar ta sanar da ranar juma’a 11 ga watan Mayu a matsayin sabuwar ranar da za’a sake gudanar da zaben fidda gwani na takarar gwamnan jihar Ekiti a karkashin jam’iyyar APC.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel