An kashe damukaradiyya kuma an birne ta Inji Sanatan da ke fada da El-Eufai

An kashe damukaradiyya kuma an birne ta Inji Sanatan da ke fada da El-Eufai

Sanatan Kaduna ta Arewa watau Sulaiman Uthman Hunkuyi ya maida martani ga tsinuwar da Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai yayi masu a wajen wani taron siyasa kwanan nan.

Gwamna Nasir El-Rufai lokacin da yake yakin yi wa Jam’iyyar APC kamfe a zaben kananan Hukumomin da za ayi a makon gobe ya bayyana cewa Sanatocin Jihar su ne Makiyan al’umman Kaduna inda ya tattara ya la’ance su.

An kashe damukaradiyya kuma an birne ta Inji Sanatan da ke fada da El-Eufai

Sanata Hunkuyi yace ba zai biyewa Gwamna El-Rufai ba

‘Dan Majalisar da yake bayani a gidan talabijin ya bayyana cewa ba zai maida martani ga zagen-zagen da Gwamnan yayi ba saboda wasu dalilai. Sanatan na APC yace wanda Ubangiji ke dafa masa ba zai fito yana fada da wani ba.

Bayan nan Sanatan ya nemi a soke zaben da aka yi a makon da ya wuce da sunan zaben shugabannin Jam’iyya a kananan Hukumomi. Sanatan yace babu wani zaben da aka yi a Kaduna a wancan makon kamar yadda aka shirya.

KU KARANTA: Sanatan Kaduna ya bayyana abin da ya sa ake kashe jama’a a Najeriya

Hunkuyi yace a gidan Gwamnati kurum aka shiga aka zauna aka fito da sunayen bogi a matsayin shugabannin APC na mazabun kananan hukumomi. Sanatan yace da sa hannun Shugaban APC na kasa John Oyegun aka yi wannan.

Kwanaki kun ji Nasir El-Rufai yayi jawabi kafin zaben inda yake cewa daga hawan su mulki zuwa yanzu babu karamar Hukumar da ba za ta iya biyan albashi ba cikin kananan Hukumomi 23 na Jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel