Sanata Shehu Sani ya koka da halin da Najeriya ke ciki

Sanata Shehu Sani ya koka da halin da Najeriya ke ciki

- Sanata Shehu Sani yayi tir da irin kashe-kashe da ake yi a Najeriya

- Sani yace ‘Yan siyasa sun maida neman kujera a-mutu ko a-yi rai

-Sanatan yace don Talakawa ake kashe shiyasa abin ya ki cinyewa

Mun samu labari cewa Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki ya bayyana cewa dole ayi maza ayi wani abu game da manyan makamai da ke fadawa hannun bata-gari.

Sanata Shehu Sani ya koka da halin da Najeriya ke ciki

Dan Majalisar APC Shehu Sani yayi magana kan sha'anin tsaro
Source: Depositphotos

Sanata Shehu Sani yake cewa Najeriya na iya shiga wani mugun yaki idan ba a karbe makamai daga tsageru ba. ‘Dan Majalisar yace ‘Yan siyasar kasar ne ke amfani da irin wadannan ‘Yan daba domin cin ma burin su.

‘Dan Majalisar yayi wannan jawabi ne lokacin da wani Takwaran sa Sanatan Kaduna ya kawo wani kudiri a Majalisar da za ta sa makamai su daina shiga hannun ‘Yan iskan gari. Sani yace dole a rika siyasa da tsabta.

KU KARANTA: An gano Sojojin Najeriya su na tserewa da 'Yan mata

Bayan nan Sanatan yace Sojoji sun tsere daga Birnin-Gwari daf da za a kai harin kwanaki bayan da su ka ga Tsagerun Yankin rike da manyan makamai. Sanatan dai ya koka da yadda ake kashe Talakawa a hare-haren.

A shafin sa na Tuwita, Sanatan ya bayyana cewa an gaza maganin kashe-kashen da ake yi a kasar saboda ta’adin na aukawa Talakawa ne da sauran Mazauna karkara inda ya nuna da ace Mala’u aka taba da an yi gyara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel