Toh fa: Fadar shugaban kasa bata san ranar da shugaba Buhari zai dawo ba daga Landan

Toh fa: Fadar shugaban kasa bata san ranar da shugaba Buhari zai dawo ba daga Landan

Fadar shugaban kasa ta sanar da cewa ba ta da tabbacin ko shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo a ranar Asabar 12 ga watan Mayu daga kasar Landan kamar yadda aka tsara, inda yaje don duba lafiyarsa.

Legit.ng ta ruwaito Kaakakin shugaban kasa, Femi Adesina ne ya sanar da haka a ranar Talata, 8 ga watan Mayu a yayin hira da yayi ta wayar tarho da gidan talabijin na Channels.

KU KARANTA: Mai martaba Sarkin Katsina ya nada sabon Babban Limamin jihar Katsina

Da aka tambayeshi idan akwai tabbacin shugaba Buhari zai dawo bayan kwanai hudu yana duba lafiyarsa a birnin Landan kamar yadda aka tsara, sai Adesina yace “Idan kana batun tabbaci ne, mutum ba zai iya bada tabbaci ba, babu wanda zai iya baka tabbaci akan wani abu.

Toh fa: Fadar shugaban kasa bata san ranar da shugaba Buhari zai dawo ba daga Landan

Tafiyarsa

“Amma muna sa ran shugaban kasar zai dawo gida Najeriya a ranar Asabar da ikon Allah, inda muke sa ran zai garzaya jihar Jigawa don ziyarar aiki na kwanaki biyu.” Inji Kaakakin.

Sai dai majiyar ta sake tambayarsa game da yanayin cutar dake damun shugaban kasa, sai Adesina yace shugaban ne kadai zai iya bayyana matsalar da yake fama da ita, sai dai yace babu abin damuwa game da lamarin, inda yace ya je ne domin a duba shi kawai.

“Wannan kuma wani abu ne na kashin kai, don kawai mutum na shugaban kasa ba yana nufin bas hi da sirri ba ne, har sai idan shugaban ne ya bayyana matsalar da yake fama da ita da kansa, do kuwa ko likitansa albarka.” Inji Femi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel