Cutar Ebola ta sake bayyana a jamhuriyyar Congo, rayuka 17 sun salwanta

Cutar Ebola ta sake bayyana a jamhuriyyar Congo, rayuka 17 sun salwanta

Kimanin rayuka 17 ne suka salwanta a yankin Arewa maso Yammacin kasar jamhuriyyar Congo, sakamakon cutar Ebola da ta sake barkewa a kwana-kwanan nan kamar yadda cibiyar lafiya ta kasar ta bayyana a ranar Talatar da ta gabata.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, kimanin mutane 11, 000 ne suka riga mu gidan gaskiya a kasashen Sierra Leone, Guinea da kuma Liberia sakamakon barkewar wannan cuta ta Ebola a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2015.

Cutar Ebola ta sake bayyana a jamhuriyyar Congo, rayuka 17 sun salwanta

Cutar Ebola ta sake bayyana a jamhuriyyar Congo, rayuka 17 sun salwanta

Wannan shine karo na tara da cutar ta barke a jamhuriyyar Congo tun gabanin kunnowar ta a shekarar 1976 inda wasu 'yan kasar Belgium suka binciko ta.

KARANTA KUMA: Fadar Shugaban Kasa ta jeranto Laifukan Rashawa a karkashin gwamnatin Jonathan

Cibiyar lafiya ta duniya watau WHO (World Health Organisation), ta tabbatar da barkewar wannan cuta a jamhuriyyar Congo bayan binciken da ta gudanar a ranar 3 ga watan Mayu.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, mutane sun fara kamuwa da rashin lafiya ta zazzabi a ranar 22 ga watan Afrilu a gundumar Bas-Uele dake Arewacin kasar a garin Kinshasha dake iyaka ta kasar Afrika ta Tsakiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel