Bango ya tsage: Saudiyya na goyon bayan Amurka a rikicinta da kasar Iran kan mallakar Nukiliya

Bango ya tsage: Saudiyya na goyon bayan Amurka a rikicinta da kasar Iran kan mallakar Nukiliya

Kasar Saudiya ta bayyana goyon bayanta dari bisa game da matakin da gwamnatin kasar Amurka ta dauka akan kasar Iran game da mallakar makamin Nukuliya da kasar Iran ta yi, kamar yadda kamfanin dillancin labaru na AFP ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kasar Amurka ta janye daga yarjejeniyar da gwamnatin tsohon shugaba Obama ta shiga da kasar Iran na cewa zata dakatar da shirinta na hada makaman Nukiliya, a shekarar 2015.

KU KARANTA: Soyayya ta koma kiyayya: Uwargida yar shekara 16 ta kashe Mijinta da maganin ɓera a jihar Kano

“Kasar Saudiyya ta goyi bayan sanarwar da Amurka ta fitar game da matakin da ta dauka na janyewa daga yarjejeniyar da kasar ta shiga da Iran a baya, tare da daura ma kasar Iran takunkumi.” Inji kasar Saudiyya.

Bango ya tsage: Saudiyya na goyon bayan Amurka a rikicinta da kasar Iran kan mallakar Nukilya

Saudi da Amurka

Kasar Saudiyya ta zargi Iran da yin amfani da kudaden da ta samu tun bayan janye takunkumin da kasar Amurka ta sanya mata a baya wajen lalata zaman lafiya a yankin Larabawa, tare da kawo rarrabe rarraben kawuna.

Rikici a tsakanin kasar Iran da kasar Amurka ba sabon abu bane, duba da cewa dukkanin kasashen biyu na bin mabanbanta sashi na addinin Musulunci ne, yayin da Saudiyya ke kan tafarkin Ahlussunnah, ita kwa Iran kasar shi’a ce.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel