Bahallatsar Dino Melaye: Kaakakin majalisa da tawagarsa sun kai masa ziyara

Bahallatsar Dino Melaye: Kaakakin majalisa da tawagarsa sun kai masa ziyara

A ranar Talata 8 ga watan Mayu ne Kaakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya jagoranci tawagar yan majalisa zuwa babban Asibiti na kasa dake babban birnin tarayya Abuja don ziyarar dubiya ga Sanata Dino Melaye, inji rahoton Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dogara ya samu rakiyar mataimakin Kaakakin majalisa, Yusuff Lasun, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Binta Bello da sauran yan majalisa,inda tsohuwar Kaakakin majalisar, Patricia Etteh ta tarbe su, da shugaban Aisibitin, Dakta Jaf Momoh.

KU KARANTA: Allah ya yi ma Dan uwan shahararren dan wasan Najeriya Rashidi Yakini rasuwa

Kaakain ya tarar da Sanatan ne a sashin kulawa da masu tsananin ciwo, inda ya same shi kwance kan gado yana samun kulawa daga cutar Asma da yake fama da ita, kuma ta taso masa sakamakon wahalar da ya sha a hannun Yansanda.

Bahallatsar Dino Melaye: Kaakakin majalisa da tawagarsa sun kai masa ziyara

Dogara da Melaye

Shi dai Sanata Melaye ya gamu da matsaloli daban daban ne kimanin satuttuka uku da suka gabata, tun a lokacin da Yansanda suka yi ram da shi, shi kuma ya subuce musu ta hanyar dirowa daga motar Yansandan da za ta kaishi garin Lokoja na jihar Kogi.

Daga karshen ziyarar, Honorabul Yakubu Dogara ya yi addu’ar Allah ya baiwa Sanata Dino Melaye lafiya, dama can Dogara ya kai korafi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari game da yadda Yansanda suka wulakanta Melaye.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel