Rikicin APC: Yan takaran gwamna 33 su shiga ganawar sirri da Tinubu, da alamun a shawo kan matsalan

Rikicin APC: Yan takaran gwamna 33 su shiga ganawar sirri da Tinubu, da alamun a shawo kan matsalan

A yanzu haka, babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, yana ganawar sirri da yan takaran gwamnan jihar Ekiti karkashin jam’iyyar guda 33 da za’ayi a watan Yuli mai zuwa.

An tattaro cewa Ganawar da akeyi a masaukin gwamnan jihar Legas da ke Asokoro, babban birnin tarayya Abuja na iya haifar da ‘da mai ido ta hanyar hada kai wajen fidda mutum daya.

Har yanzu suna cikin ganawar da aka dade da farawa.

Jami’yyar APC ta shirya zaben fidda gwanin tsakanin yan takaranta 33 a ranan Asabar, 6 ga watan Mayu amma rikici ya balle a wajen zaben. Yanzu an daga zaben zuwa ranan Juma’a, 11 ga watan Mayu.

Rikicin APC: Yan takaran gwamna 33 su shiga ganawar sirri da Tinubu, da alamun a shawo kan matsalan

Rikicin APC: Yan takaran gwamna 33 su shiga ganawar sirri da Tinubu, da alamun a shawo kan matsalan

Kakakin jam’iyyar APC, Malam Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa wajibi ne ga kowani wakilin dan takara da zai zo ranan Juma’a ya rataye takarda dauke da sunan wanda yake wakilta domin gane ainihin wadanda suka haddasa rigima.

KU KARANTA: Ina gwanin wani ga nawa: Wani hamshakin Farfesan jami’ar ABU ya samar da maganin zazzabin cizon Sauro

Kana kuma sun kara yawan jami’an yan sanda wadanda zasu taimaka wajen tabbatar da tsaro a ranan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel