Jami’an ‘Yan Sanda sun ceci Shugaban Jam’iyyar APC a Ekiti

Jami’an ‘Yan Sanda sun ceci Shugaban Jam’iyyar APC a Ekiti

- Zaben shugabannin Jam’iyyar APC ya tashi babu dadi a Ekiti

- An tsere da shugaban Jam’iyyar Jihar domin kar ayi masa illa

- Magoya bayan tsohon Gwamna Dr. Fayemi sun yi zanga-zanga

Mun samu rahoto daga manema labarai cewa zaben shugabannin Jam’iyyar APC a Jihar Ekiti ya tashi da rikici har ta kai Jami’an tsaro sun shigo sakatariyar Jam’iyyar har su ka rufe ofisoshin.

Jami’an ‘Yan Sanda sun ceci Shugaban Jam’iyyar APC a Ekiti

An tashi da rikici wajen zaben kananan Hukumomin APC a Ekiti

Zaben shugabannin kananan hukumomin Jam’iyyar APC ya zo da rikici bayan da magoya bayan Ministan Ma’adanai kuma tsohon Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi su kayi yunkurin tsige Shugaban Jam’iyyar Jihar Awe Jide.

Wasu ‘Yan Jam’iyyar APC mau mulki sun koka da yadda aka gudanar da zaben makon jiyan. Tsohon Gwamnan na Ekiti Dr. Kayode Fayemi yana cikin masu harin kujerar Gwamnan Jihar na Ekiti a zaben bana da ake shirin yi.

KU KARANTA: An zargi Shugaban APC Oyegun da hura wutan-rikicin Jam’iyya

Wadanda ke tare da tsohon Gwamnan sun yi kira a tsige Shugaban Jam’iyyar Jide Awe wanda ya sha da kyar a wajen zaben. Jami’an ‘Yan Sanda ne su ka tsere da Awe domin gudun a ga bayan sa. Yanzu dai ana ta faman rikici a Jam’iyyar.

Kuma kun ji cewa an nemi a tashi jina-jina wajen zaben da aka shirya na shugabannin Jam’iyyar APC a kananan Hukumomin da ke fadin kasar a Jihar Imo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel