An fara Gwamnati ta sa dokar ta-baci a Jihar Kaduna

An fara Gwamnati ta sa dokar ta-baci a Jihar Kaduna

- An fara kokawa da halin tsaron da ke Yankin Kudancin Kaduna

- Kungiyar HURIWA ta nemi a fara maganar tsige Shugaba Buhari

- Haka kuma HURIWA ta kuma soki Majalisar dokoki na Kaduna

Wata Kungiya da ke kula da hakkin Jama’a a Najeriya watau HURIWA ta bayyana cewa ya kamata a tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari a dalilin kashe-kashen da ake yi a cikin kasar nan musamman a Yankin Birnin-Gwari.

An fara Gwamnati ta sa dokar ta-baci a Jihar Kaduna

HURIWA tace Majalisa ta tsige Shugaban kasa Buhari

Kungiyar HURIWA ta koka bayan da aka kashe dinbin jama’a a Garin Birnin Gwari a kwanakin baya. Kungiyar ta kuma nemi Gwamnatin Tarayya ta sa dokar ta-baci a Yankin na Birnin Gwari da bangaren Kudancin Najeriya.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya tattara ya wuce Landan ganin Likita

Shugaban Kungiyar Kwamared Emmanuel Onwubiko yake cewa idan har Shugaba Buhari ba zai yi maganin kashe-kashen da Makiyaya ke yi a fadin kasar ba yayi murabus ko kuma Majalisar Tarayyar kasar ta tsige shi.

HURIWA ta ke cewa da ban mamaki ace duk da yawan makaman yakin da ke Jihar Kaduna amma ana ta’adi a Jihar. Kungiyar ta kuma soki Majalisar dokokin Jihar Kaduna saboda sakacin da tayi a bangaren tsaro a Jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel