Sanata ya zargi 'yan siyasa a kan shigar miyagun makamai hannun farar hula

Sanata ya zargi 'yan siyasa a kan shigar miyagun makamai hannun farar hula

Sanatan jami'iyyar APC mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya Zargi 'yan siyasan Najeriya da laifin yada muggan makamai a hannun farar hula a sassan daban-daban na Najeriya.

Sanatan ya furta hakan ne yayin da yake tofa albarkacin bakinsa kan wata kudiri a kan yaduwar makamai a Najeriya wanda Sanata Suleiman Hunkuyi na jami'iyyar APC mai wakiltan Kaduna North ya gabatar gaban Majalisa.

Hunkuyi ya koka kan yadda ake yiwa mutane kisan kiyashi a wasu sassan Najeriya inda yayi misali da kashe-kashen da akayi a ranar Asabar da ta gabata a jihar Kaduna.

Sanata ya zargi 'yan siyasa a kan shigar miyagun makamai hannun farar hula

Sanata ya zargi 'yan siyasa a kan shigar miyagun makamai hannun farar hula

KU KARANTA: Amurka ta gindaya wasu ka'idoji kafin ta dawo da kudaden Abacha ya karkatar

Harin da wasu yan bindiga suka kai garin Gwaska da ke karamar hukumar Birnin Gwari ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 58. An kai harin ne kwanaki biyu bayan Sufetan yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris da babban kwamandan 1 Division na Sojin Najeriya, Mohammed Mohammed sun ziyarci karamar hukumar.

Yan bindigan kuma sun kashe Sarkin Fawa (Shugaban yan banga) a hanyar sa na dawowa kauyen tare da kona gidaje da dama a kauyen da ke da yawan mutane sama da 3,000.

Bayan harin, gwamna Nasir El-Rufai ya bayar da sanarwan cewa gwamnatin tarayya ta amince da kafa bataliyan sojoji a yankunan da ake kai hare-haren.

A jawabinsa, Mr. Sani ya nuna rashin jin dadin sa kan yadda Majalisar ke yawan gayyatar shugabanin hukumomin tsaro don su bayar da bayanai. Ya ce babban matsalar shine yadda yan siyasa ke siyo makamai kuma su danka su hannun farar hula.

A cewarsa, bindigogin da ke hannun mutane sun fi taraktan ayyukan noma yawa kuma hakan ne ke kara tabarbarwar zaman lafiya a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel