Na zaci zaka gyarawa Trump zancansa cewa ba kiristoci kadai ake kashewa ba a Najeriya – Dan majalisa ga Buhari

Na zaci zaka gyarawa Trump zancansa cewa ba kiristoci kadai ake kashewa ba a Najeriya – Dan majalisa ga Buhari

- Aliyu Madaki mamba a majalisar wakilai, ya shawarci Donald Trump da kada ya kawowa Najeriya irin siyasarsa ta rarraba kawuna

- Ya bayyana hakan ne a ranar Talata bayan Donald Trump ya karbi bakuncin shugaba Muhammadu Buhari a satin da ya gabata

- Trump ya fadawa Buhari cewa kasar Amruka bazata amince da kisan kiristoci a Najeriya ba, lokacin da suke ganawa a kasar ta Amurka

Aliyu Madaki mamba a majalisar wakilai, ya shawarci Donald Trump da kada ya kawowa Najeriya irin siyasarsa ta rarraba kawuna.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata bayan Donald Trump ya karbi bakuncin shugaba Muhammadu Buhari a satin da ya gabata.

Na zaci zaka gyarawa Trump zancansa cewa ba kiristoci kadai ake kashewa ba a Najeriya – Dan majalisa ga Buhari

Na zaci zaka gyarawa Trump zancansa cewa ba kiristoci kadai ake kashewa ba a Najeriya – Dan majalisa ga Buhari

Trump ya fadawa Buhari cewa kasar Amurka bazata amince da kisan kiristoci a Najeriya ba, lokacin da suke ganawa a kasar ta Amruka. Yayinda shugaba Buhari ya fada masa cewa gwamnati na iya gwargwadon kokarinta don ganin ta magance kisan da akyi a fadin kasar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisa ta gayyaci shugabannin tsaro, bisa ga mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba da mutane keyi a Najeriya

Lokacin da ake zancan a majalisa Madaki yace ya zaci shugaba Buhari zai “gyarawa” shugaban kasar na Amurka maganarsa na cewa ba kiristoci kadai ake kashewa ba a Najeriya.

Dan majalisar yace shugaba Trump “sananne ne ta fannin kabilanci da nuna banbanci da son rai da kuma hargitsi”, ya kara da cewa bazasu bari Trump ya kawo siyasar ra’ayinsa ba a Najeriya.

A halin da ake ciki, Femi Adesina a ranar Talata yace Buhari kadai keda hurumin bayar da bayani game da lafiyar jikinsa sai shi shugaba Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel