Buhari kadai keda damar bayyana lafiyarsa - Adesina

Buhari kadai keda damar bayyana lafiyarsa - Adesina

- Femi Adesina a ranar Talata yace Buhari kadai keda hurumin bayar da bayani game da lafiyar jikinsa

- Mai bawa shugaban kasar shawara akan sadarwa ya bayyana hakan ne sakamakon tambayar da akayi masa game da tafiyar Buhari Landon domin duba lafiyarsa

- Babban mataimakin shugaban kasar garba Shehu ya bayyana tafiyar shugaban kasar zuwa kasar Ingila na tsawon kwanaki hudu domin ganin Likitansa

Femi Adesina a ranar Talata yace Buhari kadai keda hurumin bayar da bayani game da lafiyar jikinsa sai shi shugaba Buhari.

Mai bawa shugaban kasar shawara akan sadarwa ya bayyana hakan ne lokacin da Channels Television ke zantawa dashi a waya, sakamakon tambayar da suka yi masa game da tafiyar Buhari Landon domin duba lafiyarsa.

Babban mataimakin shugaban kasar garba Shehu ya bayyana tafiyar shugaban kasar zuwa kasar Ingila na tsawon kwanaki hudu domin ganin Likitansa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisa ta gayyaci shugabannin tsaro, bisa ga mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba da mutane keyi a Najeriya

Mai magana da yawun shugaban kasar yace game da tafiyar shugaban kasar Landon, yana dawowa zai ziyarci jihar Jigawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel