Fadar Shugaban Kasa ta jeranto Laifukan Rashawa a karkashin gwamnatin Jonathan

Fadar Shugaban Kasa ta jeranto Laifukan Rashawa a karkashin gwamnatin Jonathan

A ranar Litinin din da ta gabata ne fadar shugaban kasa ta tunkari tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan gami da kalubalantar sa da laifukan rashawa da suka afku a lokacin gwamnatin sa.

Tsohon Shugaban kasa; Goodluck Jonathan

Tsohon Shugaban kasa; Goodluck Jonathan

Babban hadimi na mataimakin shugaban kasa akan hulda da manema labarai, Mista Laolu Akande, shine ya yi wannan fashin baki yayin ganawa da manema labarai a birnin Abuja.

Akande dai ya bayyana cewa, ya yi wannan fashin baki domin mayar da martani ga tsohon shugaban kasa akan karyata batun laifukan rashawa da suka afku a gwamnatin sa.

A makon da ya gabata mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yayi ikirarin cewa mutane uku kacal sun yi sama da fadi da zunzurutun kudi har na Dalar Amurka biliyan uku a lokacin tsohuwar gwamnatin ta Jonathan.

KARANTA KUMA: Wani 'Da ya kashe Mahaifinsa mai shekaru 83 a duniya a jihar Enugu

A yayin tabbatar da wannan ikirari kamar yadda mataimakin shugaban kasar ya bayyana, Mista Laolu yace ko shakka babu mutane ukun sun hadar da; Jide Omokere, Kola Aluko da kuma tsohuwar ministan man fetur, Diezani Alison-Maduekwe da suka wawushe asusun kamfanin man fetur na kasa watau NNPC.

Babban hadimin ya kuma bayyana yadda aka wawushe kudin makamai da aka nufaci saye domin yakar ta'addancin Boko Haram har na Dalar Amurka Biliyan 2.5 duk a lokacin tsohuwar gwamnati.

Akwai kuma Dalar Amurka Miliyan 289 da aka wawushe cikin asusun kamfanin man fetur na kasa a ranar 25 ga watan Fabrairu na 2015.

Baya ga wannan akwai kuma Naira biliyan 70 da aka tatse daga asusun gwamnatin tarayya a tsakanin ranar 8 ga watan Janairu da kuma 25 ga watan Fabrairun 2015.

Cikin wani magudin kuma da aka gudanar a karkashin hukumar NSA, an yi sama da fadi da Naira biliyan 60 a ranar 25 ga watan Agusta na 2014.

KARANTA KUMA: Takaddamar Maganin Tari: Hukumar NAFDAC ta datse kamfanoni 3 a Kudancin Najeriya

Kakakin fadar shugaban kasar ya ci gaba cewa, akwai kuma rashawa ta Naira Biliyan 1.5 da aka wawushe cikin mako guda a tsakanin ranar 8 da 16 ga watan Janairun 2015.

Wata shaidar takardu ta kuma bayyana yadda babban bankin Najeriya ya malalo Naira Biliyan 10 a ranar 15 ga watan Satumba na 2014 zuwa ga ofishin hukumar NSA wanda Kanal Sambo ke jagoranta a lokacin tsohuwar gwamnatin.

Cikin cikon tabbacin rashawa da ta afku a lokacin shugabancin Jonathan, babban hadimin ya bayyana yadda aka yi magudin sallamar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Lamido Sanusi sakamakon fallasa rashawar Dalar Amurka Biliyan 20 da aka aiwatar cikin kudin man fetur na kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel