An gano dalilin da yasa yaki da cin da Buhari keyi baya samun nasara

An gano dalilin da yasa yaki da cin da Buhari keyi baya samun nasara

Babban limamin rukunin Cocin Rain Assembly, Fasto Tunde Bakare, ya bayyana fahimtar sa a kan dalilan da suka sanya yakin da Buhari keyi da cin hanci baya samun nasara.

Fasto Bakare ya bayyana cewar gwamnatin tarayya bata bind hanyoyin da suka dace domin samun nasara a kan wadanda aka samu da laifukan cin hanci.

A shekarar 2oi7 ne wata kungiyar saka idanu ta duniya a kan yaki da cin hanci ta saka Najeriya cikin sahun kasashen da suka gaza tabuka rawar gani a yaki da cin hanci.

An gano dalilin da yasa yaki da cin da Buhari keyi baya samun nasara

Magu da Buhari

A wani shirin gidan Talabijin na Channels mai taken Roadmap 2019, Bakare, ya bayyana cewar gwamnatin shugaba Buhari bata yakar cin hanci ta hanyar da zata kai ta ga nasara.

Bakare ya kara da cewa, a yayin da gwamnatin ke matsawa wasu da ake tuhuma da laifin cin hanci, wasu kuma ana nuna masu sassauci ko hannun ya san na gida.

DUBA WANNAN: Kotu ta umarci PDP ta biya lauyan da ya yi mata aiki kudin sa miliyan N180m

Bakare ya ce shugaba Buhari ya gaza cika alkawuran da ya yiwa 'yan Najeriya tare da bayyana damuwar sa bisa kisan mutanen jihar Benuwe da har yanzu gwamnatin ta gaza dakatarwa.

"Wadannan hare-hare manuniya ce cewar akwai bukatar mu tattauna kasancewar mu a matsayin kasa daya, al'umma daya," a cewar Tunde Bakare.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel