Hukumar 'Yan sanda ta tabbatar da kai hari a Gidan wani Mai Gari a jihar Filato

Hukumar 'Yan sanda ta tabbatar da kai hari a Gidan wani Mai Gari a jihar Filato

A ranar Talata ta yau ne hukumar 'yan sanda ta jihar Filato ta tabbatar da afkuwar hari da 'yan ta'adda suka gudanar a gidan John Dalyop, mai garin Gashish dake karamar hukumar Riyom ta jihar.

Kakakin hukumar, ASP Terna Tyopev, shine ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da 'yan jarida na kafar watsa labarai ta NAN a birnin Jos da cewar tabbas wannan hari ya afku ne da misalin karfe 10.00 na daren ranar Lahadin da ta gabata.

Tyopev ya bayyana cewa an yi babbar nasara wannan hari sakamakon rashin salwantar rayuka in banda na kone gida da kuma motar hawa mallakin mai garin na Gashish.

Hukumar 'Yan sanda ta tabbatar da kai hari a Gidan wani Mai Gari a jihar Filato

Hukumar 'Yan sanda ta tabbatar da kai hari a Gidan wani Mai Gari a jihar Filato

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan 'yan ta'adda dauke da makamai na bindigu wanda kawowa yanzu ba bu wata masaniya a kansu sun kone gida da kuma wata mota kirar Peugeot 406 kurmus yayin aiwatar da harin.

Rahotanni sun bayyana cewa, anyi gaggawar garzayawa da mai garin zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Jos sakamakon dimuwa da ta damkeshi a sanadiyar wannan hari.

KARANTA KUMA: An sake yiwa Buratai Karamci na Gwarzon Jagora

Kakakin hukumar 'yan sandan ya kara da cewa, tuni al'ummar yankin sun ci gaba da gudanar da harkokin su kuma bincike ya ci gaba da kankama domin bankado wannan miyagu.

Ya kuma nemi mazauna wannan yanki akan su ci gaba da gudanar da al'amurransu cikin kwanciyar hankali kuma su kasance masu kiyaye doka da yi mata da'a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel