Amurka ta gindaya wasu ka'idoji kafin ta dawo da kudaden Abacha ya karkatar

Amurka ta gindaya wasu ka'idoji kafin ta dawo da kudaden Abacha ya karkatar

- Kasar Amurka ta fadawa shugaba Buhari cewa ba za ta amince da wasu masu shiga tsakani ba wajen maido da kudin Abacha ya ajiye a kasar

- An gano kudaden ne tun zamanin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan amma aka ajiye su a kasar Amurka

- Ministan kudi, Kemi Adeosun ta tabbatar wa 'yan Najeriya cewa dalla miliyan 322.51 da zaka karba zai tafi asusun tallafawa al'umma Najeriya ne

Gwamnatin kasar Amurka ta ce ba zatayi hulda da wasu dillalai ba sai dai gwamnatin Najeriya kawai wajen tattauna yadda za'a dawo da dallan Amurka miliyan 500 da tsohon shugaban mulkin Soja, Sani Abacha ya ajiye a kasashen ketare.

Amurka ta gindaya wasu ka'idoji kafin ta dawo da kudaden Abacha ya karkatar

Amurka ta gindaya wasu ka'idoji kafin ta dawo da kudaden Abacha ya karkatar

Jaridar Cable ta ruwaitp cewa wata majiya daga fadan shugaban kasa ta ce Sashin Shari'ah na kasar Amurka (DOJ) ta fadawa shugaba Buhari yayin da ya ziyarci Amurka cewa ba su son a tsunduma wasu mutane cikin batun mayar da kudaden na Abacha.

KU KARANTA: An kara kama shi da laifin fashi da makami kwana 25 da sakin sa daga gidan yari

Attorney Janar na kasa, Abubakar Malami, ya yi yunkurin daukan hayar wasu lauyoyi masu zaman kansu don su taimaka wajen dawo da kudaden zuwa Najeriya.

Za'a ware wa lauyoyin wani koso cikin kudin a matsayin la'adan aikinsu duk da cewa basu taka wata rawa ba wajen fafutikar gano kudaden da tsohon shugaban mulkin sojin ya karkatar zuwa kasashen wajen.

An dai gano kudaden ne a shekarar 2014 karkashin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan sannan aka ajiye kudaden a kasar Amurka. Kazalika, an biya lauyoyin da sukayi aikin gano kudin hakkin su na 4% cikin kudin.

Za'a dawo da kudaden ne bayan gwamnatin tarayya ta sanya hannu a kan wata yarjejeniya na amincewa ba za'a yi almubazaranci da kudaden ba kamar yadda akayi da kudaden da aka dawo wa Najeriya da su karkashin mulkin Olusegun Obasanjo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel