Kotu ta tursasa PDP biyan lauya Naira miliyan N180m kudin aikin da ya yi masu

Kotu ta tursasa PDP biyan lauya Naira miliyan N180m kudin aikin da ya yi masu

- Mai shari'a Jude Okeke na babbar kotu dake Maitama, Abuja, ta umarci jam'iyyar PDP ta biya lauya, Samuel Okutepa, kudin aikin sa miliyan N180m

- Alkalin kotun ya yanke wannan hukunci ne a yau, Talata, bayan lauya Okutefa ya shigar da karar jam'iyyar saboda ta ki biyan sa wasu kudin aiyukan da ya yi mata

- Saidai jam'iyyar PDP ta musanta cewar bata bashi kowanne aiki ba domin babu wata shaidar yarjejeniya tsakanin su

Mai shari'a Jude Okeke na babbar kotu dake Maitama, Abuja, ta umarci jam'iyyar PDP ta biya lauya Samuel Okutepa, kudin aikin sa miliyan N180m

Alkalin kotun ya yanke wannan hukunci ne a yau, Talata, bayan lauya Okutefa ya shigar da karar jam'iyyar saboda ta ki biyan sa wasu kudin aiyukan da ya yi mata.

Kotu ta tursasa PDP biyan lauya Naira miliyan N8m kudin aikin da ya yi masu

Shelkwatar jam'iyyar PDP ta kasa

"Dole wanda ake kara ya biya lauya kudin aiyukan sa da ya yi masu na kare jam'iyyar a kotu a wasu shari'o'i da ya lissafa a cikin takardar karar," a cewar mai shari'a Okeke.

Kazalika kotun ta umarci PDP da ta biya Mista Okutepa N50,000 bisa kyakykyawan aikin da ya yi mata tare da bayyana cewar kuskure ne jam'iyyar ta PDP ta ki biyan kudin aikin sa duk da cewar ya kai su ga nasara a shari'o'in da ya kare ta.

DUBA WANNAN: APC zata haramtawa wasu 'ya'yan ta tsayawa takarar gwamna

Saidai jam'iyyar PDP ta musanta cewar bata bashi kowanne aiki ba domin babu wata shaidar yarjejeniya tsakanin su.

Saidai lauyan ya gabatar da shaidar wani aiki da tsohon gwamnan jihar Benuwe, Gabriel Suswan, ya saka shi a madadin jam'iyyar PDP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel