Yanzu Yanzu: Majalisa ta gayyaci shugabannin tsaro, bisa ga mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba da mutane keyi a Najeriya

Yanzu Yanzu: Majalisa ta gayyaci shugabannin tsaro, bisa ga mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba da mutane keyi a Najeriya

- Majalisa ta yanke shawarar gayyatar duka jagororin Najeriya da Lawal Daura na ‘Yan Sandan ciki, da kuma Hameed Ali na Kwastam, bisa ga mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba

- Majalisar ta yanke shawarar gayyatosu ne bayan korafi da aka gabatar mata game da magance mallakar makamai ba bisa ka’ida ba Najeriya wanda Sulaiman Hunkuyi ya gabatar

- Jami’an tsaron zasu bayar da shawarwari game da yanda za’a mangance wannan matsala dake damun Najeriya

Majalisa ta yanke shawarar gayyatar duka shugabannin tsaro na Najeriya da Lawal Daura na ‘Yan Sandan ciki, da kuma Hameed Ali na Kwastam, bisa ga mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba da al'umman kasar ke yi.

Majalisar ta yanke shawarar gayyatosu ne bayan korafi da aka gabatar mata game da magance mallakar makamai ba bisa ka’ida ba Najeriya wanda Sulaiman Hunkuyi na jam’iyyar APC mai wakiltar Kaduna ta arewa ya gabatar.

Yanzu Yanzu: Majalisa ta gayyaci shugabannin tsaro, DG-SSS, CG-Customs, bisa ga mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba da mutane keyi a Najeriya

Yanzu Yanzu: Majalisa ta gayyaci shugabannin tsaro, DG-SSS, CG-Customs, bisa ga mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba da mutane keyi a Najeriya

Jami’an tsaron zasu bayar da shawarwari game da yadda za’a mangance wannan matsala dake damun Najeriya.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kai tallafi ga al’umman karamar hukumar Mubi da harin Boko Haram ya rutsa da su indaya bayar da gudunmawar naira miliyan 10.

KU KARANTA KUMA: Hanyoyin 5 da zaka dawwamar da soyayyarka a zuciyar matarka

Atiku ya danka wannan kudi ne a wata asusu na tallafi dake karkashin ikon asibitin gwamnatin tarayya dake Yola mai suna (Yola’s Paupers Funds’) domin tallafawawadanda ke kwance a asibitin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel