Atiku Abubakar ya ja hankalin Shugaba Buhari kan sha’anin tsaro

Atiku Abubakar ya ja hankalin Shugaba Buhari kan sha’anin tsaro

- Babban ‘Dan takarar Shugaban kasa Atiku yayi kira ga Buhari

- ‘Dan siyasar ya nemi Gwamnatin Tarayya ta tashi tsayin daka

- Atiku Abubakar yace za a ga karuwa laifi iri-iri yanzu a Kasar

Mun samu labari daga Jaridun kasar nan cewa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya gargadi Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari game da abin da ya shafi maganar tsaro ya kuma bada shawarwari.

Atiku Abubakar ya ja hankalin Shugaba Buhari kan sha’anin tsaro

Atiku Abubakar ya ba Gwamnatin Tarayya shawara

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriyan yace yayin da aka kama hanyar shirin zaben 2019 za a samu karuwar ta’addanci a kasar inda yayi kira ga Gwamnatin Buhari ta tashi tsaye domin shirya maganin wannan matsala.

Wazirin na Adamawa Atiku yace fashi da makami da satar jama’a zai yi kamari don haka ya ba Gwamnatin Tarayyar shawarar ta inganta harkar tsaro. Alhaji Atiku Abubakar ya nemi ayi wa Ma’aikatan tsaro a kasar sauyin aiki.

KU KARANTA: Yadda Jonathan ya saci kudin za su isa a biya albashin shekara daya a kwana guda

Atiku ya nemi a daina jefa Sojoji cikin sha’anin tsaron kasar inda ya nemi a bunkasa ‘Yan Sanda da sauran Jami’an tsaro. Atiku ya kuma nemi a ba ‘Yan Sanda makaman aiki a kuma horar da sauran Jami’an tsaro domin a samu zaman lafiya.

Atiku yayi wannan jawabi ne lokacin da ya kai ziyara ga wadanda bam ya tashi da su a Garin Mubi inda ya ba su gudumuwar kudi har Naira Miliyan 10.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel