Tonon silili: Osinbajo ya bayyana irin satar da Jonathan ya tafka a Gwamnati

Tonon silili: Osinbajo ya bayyana irin satar da Jonathan ya tafka a Gwamnati

- Mataimakin Shugaban kasa ya fasa kwan tsohon Shugaban kasa Jonathan

- Farfesa Yemi Osinbajo yace an saci Biliyan 88 a rana guda a lokacin PDP

- Wannan kudi sun isa a biya Ma’aikatan N-Power albashi na shekara guda

Mun samu labari cewa fadar Shugaban kasa ta fasa kwan irin satar da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya tafka lokacin yana Gwamnati inda tace satar dukiyar jama'a babban barazana ga tattalin arzikin kasar nan.

Tonon silili: Osinbajo ya bayyana irin satar da Jonathan ya tafka a Gwamnati

Mataimakin Shugaban kasa ya tona asirin Jonathan

The Cable ta rahoto cewa Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yace Jonathan yayi wa baitul-malin Najeriya karkaf lokacin yana kan kujera. A cewar Mataimakin Shugaban kasar, an saci sama da Naira Biliyan 80 a rana guda a lokacin mulkin Jonathan.

KU KARANTA: Mataimakin Shugaban kasa ya tona mutane 3 da su kayi barna

Mai magana da yawun Mataiamin Shugaban kasar watau Laolu Akande yace wsannan Biliyan 88 da aka yi gaba da su dai sun isa a dauki wadanda su ka kammala karatu sama da 244, 000 a biya su albashi na shekara guda a tsarin N-Power na wannan Gwamnati.

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo yana kan bakan sa ne da yace wasu mutane 3 kurum a lokacin Jonathan sun saci akalla Dala Biliyan 3 wanda wannan kudi ya haura Naira Tiriliyan 1. Kasafin Najeriya dai ba ya wuce Naira Tiriliyan 7 a shekara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel