Yadda ganawar da Shugaba Buhari da Saraki da Dogara ta kare

Yadda ganawar da Shugaba Buhari da Saraki da Dogara ta kare

Mun samu labarin abin da shugabannin Majalisar Tarayyar kasar nan su ka tattauna da Shugaba Buhari a jiya. Bayan nan ne Shugaban kasar ya bayyana cewa zai wuce Birnin Landan domin ya ga Likitan sa.

Ga dai abubuwan da manyan kasar su ka tattauna kamar yadda Hadiman Shugaba Buhari su ka bayyana:

1. Kasafin kudi

A jiya ne kundin kasafin kudin Najeriya ya cika watanni 6 a hannun Majalisar amma ba a amince da shi ba don haka Shugaban Kasar ya nemi ganawa da Shugabannin Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.

KU KARANTA: Malaman addini sun fara kokawa da abin da yake faruwa da Dino Melaye

https://hausa.legit.ng/1167891-kasurgumin-shehin-kirista-yayi-tir-da-abin-yan-sanda-ke-yi-wa-sanata-melaye.html#1167891

2. Maganar Dino Melaye

Bayan nan kuma Shugabannin Majalisar kasar sun yi wa Shugaba Buhari magana game da yadda ‘Yan Sanda ke binciken Sanatan kasar Dino Melaye. Dogara da Saraki sun nemi Shugaban kasar ya shiga tsakanin rikicin ‘Yan Sanda da ‘Dan Majalisar.

3. Batun Majalisa

Haka kuma manyan kasar sun tattauna game da batun Majalisar Najeriya wanda kwanaki aka yi kokarin fara shirin tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari a dalilin sayen wasu kayan yaki ba tare da neman iznin Majalisar Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel