Tubalin ginin APC zai rushe a hannun Oyegun – Inji ‘Dan takarar Gwamna

Tubalin ginin APC zai rushe a hannun Oyegun – Inji ‘Dan takarar Gwamna

- Wani babban ‘Dan APC ya zargi John Oyegun da kokarin kawo rikici

- Julius Ucha ya nemi a takawa Shugaban Jam’iyyar burki tun da wuri

- Sanata Ucha ya zargi Majalisar Oyegun da yunkurin kifar da Buhari

Mun samu labari cewa wani babba a Jam’iyyar APC mai mulki ya zargi Shugaban Jam’iyyar John Oyegun da kokarin kawowa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Jam’iyyar mai mulki matsala.

Tubalin ginin APC zai rushe a hannun Oyegun – Inji ‘Dan takarar Gwamna

Ana zargin Majalisar Oyegun da rikita APC

‘Dan takarar Gwamnan Jihar Ebonyi a karkashin Jam’iyyar APC Sanata Julius Ali-Ucha ya fadawa manema labarai cewa Majalisar John Oyegun na kokarin kawowa Shugaban kasa Buhari da Jam’iyyar su ta APC tasgaro.

KU KARANTA: Kan APC ya kara rabuwa wajen zaben shugabannin Jam'iyya

Julius Ali-Ucha ya bayyana wannan ne a karshen makon da ya gabata inda aka yi zaben shugabannin Jam’iyyar a fadin kasar. Sanata Ali-Ucha ya nemi manyan Jam’iyyar su sa baki a takawa Shugaba Oyegun da mutane sa burki.

Babban ‘Dan Jam’iyyar yayi tir da zaben shugabannin da aka yi a makon jiya inda yace ba a bi ka’ida ba don haka yace tubulin Jam’iyyar na iya rushewa. Sanata Ucha dai yace an yi ba dai-dai ba wajen zaben Jam’iyyar mazabu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel